Rashin tsaro ne ke tsotse mana albarkatunmu – Buhari

Rashin tsaro ne ke tsotse mana albarkatunmu – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace rashin tsaro na kara sanya matsin lamba akan albarkatun gwamnatin tarayya.

Buhari ya fadi hakan ne a Owerri, babbar birnin jihar Imo a jiya Alhamis, 2 ga watan Mayu a taron kulla yarjejeniyar zaman lafiya na kafin zabe a kudu maso gabas wanda kungiyar sarakunan gargajiya na Najeriya suka shirya.

Ya nuna bakin cikin cewa lamarin, wanda gwamnatinsa tayi nasarar yaka a farkon wa’adinsa, ya sake tabarbarewa.

Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin babban sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, yace tun bayan kammala zabe, abunda Najeriya ke bukata a yanzu shine farfadowa.

Rashin tsaro ne ke tsotse mana albarkatunmu – Buhari

Rashin tsaro ne ke tsotse mana albarkatunmu – Buhari
Source: Twitter

Yace zai ci gaba da yin duk abunda ya kamata domin tabbatar da zaman lafiya a kasar.

KU KARANTA KUMA: Abun bakin ciki ne yadda likitoci ke barin Najeriya – Ministan lafiya

Shugaban kasar ya bukaci yan Najeriya da kada su cire tsammani, cewa lamarin ba dawamamme bane kuma kwanan nan komai zai zo karshe.

Buhari ya bukaci sarakunan gargajiya da kada su yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da warzuwan zaman lafiya a kasar.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Kungiyar Jama’atil Izalatil bidi’a wa iqamatissunnah ta gargadi miyagu masu satar mutane babu gaira babu dalili da nufin karbar kudin fansa dasu tuba zuwa ga Allah ko kuma su sha ruwan Al-qunuti daga bakin Malaman kungiyar.

Kungiyar ta bayyana haka ne ta bakin shugabanta, Sheikh Sani Yahaya Jingir yayin taron bude wani katafaren Masallacin Juma’a da aka gina akan dutsen Zainariya dake garin Jos na jahar Filato a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel