Wani dan sanda ya maka abokinshi a kotu saboda ya kasa yiwa matarsa ciki, wanda ya basu damar kwanciya har sau 77

Wani dan sanda ya maka abokinshi a kotu saboda ya kasa yiwa matarsa ciki, wanda ya basu damar kwanciya har sau 77

Wani jami'in dan sanda da likitoci suka tabbatar da baya haihuwa ya baiwa abokinshi damar kwanciya da matarsa har na tsawon watanni goma, akan yarjejeniyar zai yi mata ciki a cikin wannan lokacin

Wani dan sanda a kasar Tanzaniyaya kai karar abokinsa, saboda ya kasa yi mata ciki, bayan ya ba shi damar kwanciya da ita sau 77.

Darius Makambako, mai shekaru 50 da matar shi mai shekaru 45, wanda ke son su samu haihuwa, sun zabi wata hanya, bayan da likita ya bayyana musu cewar ba zai iya haihuwa ba. Dan sandan da matar shi wanda suka shafe shekaru 6 ba tare da sun samu haihuwa ba, ya zabi makwabcinsa Evans Mastano, mai shekaru 52, akan ya kwanta da matar tasa domin ya yi mata ciki.

Wani dan sanda ya maka abokinshi a kotu saboda ya kasa yiwa matarsa ciki, wanda ya basu damar kwanciya har sau 77

Wani dan sanda ya maka abokinshi a kotu saboda ya kasa yiwa matarsa ciki, wanda ya basu damar kwanciya har sau 77
Source: Facebook

Makambako ya biya Mastano kudi kimanin TZS 2,000,000, wanda ya yi daidai da naira dubu dari uku a kudin Najeriya, akan ya kwanta da matar ta shi na tsawon kwanaki uku a kowanne sati, har sai sun cinye watanni goma a haka. Sai dai kuma Mastano ya kasa yi wa matar ciki bayan ya kwanta da ita har sau 77. Daga baya dai an gano cewa shima Evans din ya na fama da matsalar rashin haihuwa.

KU KARANTA: Surukin Dogarin Buhari: 'Yan Sanda sun yi alkawarin bayar da miliyan biyar ga wanda ya kawo labari

Sanarwar likitan da ke nuna cewa Evans Mastanno ba ya haihuwa ya firgita kowa da kowa musamman ma matarsa, wacce ta bayyana cewa Evans ba shine ainihin uban 'ya'yansu ba, dan uwanshi ne Edward ya dinga kwanciya da ita har ta samu ciki dashi.

Dan sandan wanda ya kai abokin nashi kara kotu akan ya kasa yiwa matarsa ciki, ya zargi Evans da yin amfani da damarshi wurin karbe mishi kudi. Daga baya dai an bayyana cewa Evans ya ki biyan Makambako kudin shi, saboda dama sun yi yarjejeniya akan ba babu tabbacin sai ya yi mata cikin idan suka kwanta tare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel