Abun bakin ciki ne yadda likitoci ke barin Najeriya – Ministan lafiya

Abun bakin ciki ne yadda likitoci ke barin Najeriya – Ministan lafiya

- Ministan lafiya, Isaac Adewole ya koka kan yadda likitocin Najeriya ke barin kasar zuwa kasashen waje

- Adewole yace bai ji dadin wannan al'amari ba ko kadan

- Ministan ya kuma koka kan gazawar gwamnatocin jiha da dama wajen dauka da ajiye likitoci a manyan asibitocinsu

Ministan lafiya, Isaac Adewole, yace bai ji dadin yadda likitoci ke barin kasar zuwa kasashen waje.

Kwanan nan ne dai ministan kwadago, Chris Ngige yace Najeriya na da isassun likitoci sannan cewa duk wanda ke da burin komawa wasu kasashen don neman mai maiko toh kofa a bude take.

Amma da yake magana a Abakaliki, babbar birnin jihar Ebonyi, a jiya Alhamis, 2 ga watan Mayu, a taron kungiyar likitoci na Najeriya, ministan lafiyan ya koka kan yawan toshewar basira a ma’aikatar lafiya.

Abun bakin ciki ne yadda likitoci ke barin Najeriya – Ministan lafiya

Abun bakin ciki ne yadda likitoci ke barin Najeriya – Ministan lafiya
Source: Facebook

Adewole, wanda ya samu wakilcin babban daraktan asibitin koyarwa na tarayya na Alex Ekwueme Abakaliki, Dr Emeka Onwe, yace: “Ban ji dadin yadda likitoci ke barin kasar zuwa wasu kasashe ba.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindigan da suka sace Magajin Garin Daura sun tuntubi iyalansa

“Za mu ci gaba da tabbatar da jin dadin ma’aikatan lafiya don ganin ya inganta.”

Ministan ya kuma koka kan gazawar gwamnatocin jiha da dama wajen dauka da ajiye likitoci, ciki harda kwararru, a manyan asibitocinsu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel