Jiragen dankaro guda 6 dauke da man fetir da kayan masarufi sun iso Najeriya

Jiragen dankaro guda 6 dauke da man fetir da kayan masarufi sun iso Najeriya

Akalla manya manyan jiragen dankaro guda shida makare fal da tataccen man fetir sun shigo Najeriya daga kasashen waje da nufin sauke kayan da suka yi dakonsu, kamar yadda hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, NPA ta bayyana.

Legit.ng ta ruwaito wadannan jiragen ruwa guda shida sun isa tashoshin jiragen Najeriya guda biyu ne dake jahar Legas, tashar Tin Can da tashar Apapa, tun a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Babar Sanata Dino Melaye ta rasu

Hukumar NPA ta bayyana cewa jirage uku daga cikin jirage shidan suna dauke ne da tataccen man fetir, yayin da sauran jirage uku suke dauke da daskararren kifi da kuma tarin sundukai makare da hajojin yan kasuwa.

Haka zalika hukumar ta kara da cewa a yanzu haka tana dakon wasu manyan jirage guda 29 daga ranar 2 ga watan Mayu zuwa 17 ga watan Mayu, wadanda suke dauke da nau’o’in kayayyakin masarufi daban daban.

A wani labarin kuma, shugaban hukumar NPA, Hajiya Hadiza Bala Usman ta samu karin daukaka bayan majalisar dinkin duniya, UN, ta nadata a matsayin mataimakiyar shugaban cibiyar majalisar dinkin duniya dake kula da sufurin jirgin ruwa ta duniya, International maritime organization, IMO.

A ranar Juma’a 10 ga watan Afrilu aka zabi Hadiza wannan mukami a taron majalisar na 43 da aka yi a birnin Landan, inda zata cigaba da rike mukamin na tsawon shekara daya, daga shekarar 2019 zuwa 2020.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel