Sabon salo: Buhari yayi sabbin nade nade guda 26 daga Landan

Sabon salo: Buhari yayi sabbin nade nade guda 26 daga Landan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nada wasu yan Najeriya 26 a kwamitin gudanarwa ta hukumar sufurin jirgin kasa ta Najeriya, NRC, wadanda hakkin tabbatar da hukumar tayi aikinta yadda ya kamata ya rataya a wuyansu.

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ne ya jagoranci nadin jagororin su 26 a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu a babban birnin tarayya Abuja, inda yace babban aikin dake gabansu shine su samar da ingantaccen tsarin aiki ga hukumar wanda yayi daidai da manufofin gwamnatin tarayya.

KU KARANTA: Babar Sanata Dino Melaye ta rasu

Legit.ng ta ruwaito Amaechi ya kalubalanci kwamitin data tabbata tsare tsarenta zasu taimaka wajen cimma manufar hukumar sufurin jirgin kasa, tare da samar da tattalin arziki mai daurewa, kamar yadda ake samu a sauran kasashen duniya.

Sai dai Amaechi ya gargadi yayan kwamitin dasu guji karakaina da shuwagabannin hukumar sufurin jirgin kasa don kauce ma duk wata matsala da zata iya tasowa a tsakaninsu wanda zata sabbaba sauka daga layi daga manufar da gwamnati ta sanya a gaba.

Daga karshe, shugaban kwamitin, Injiniya Ibrahim Alhassan yayi jawabi a madadin sauran yayan kwamitin 25, inda ya baiwa Minista Amaechi tabbacin yin aiki tukuru don cimma dukkanin muradu da kuma manufofin hukumar.

A wani labarin kuma, minista Amaechi ya bayyana cewa daga watan Yuni Najeriya zata karbi sabbin taragogin jirgin kasa guda goma daga kasar China, wanda ta bayar da kwangilarsu don amfani dasu akan layin dogo na Kaduna zuwa Abuja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel