Yadda ‘yan bindiga suka sace surukin Buhari a Daura

Yadda ‘yan bindiga suka sace surukin Buhari a Daura

-Yan bindiga sun sace Magajin garin Daura har gidansa

-Wannan lamarin dai ya aukune jim kadan bayan Magajin gain na Daura ya dawo daga masallacin inda yaje yin sallar magariba

Wani babban mai rike da sarautar gargajiya a masauratar Daura dake jihar Katsina wato Alhaji Musa Umar Uba shine akayi awon gaba dashi a daren Laraba a gidansa dake Daura.

Alhaji Musa Umar Uba dai shine ke rike da sauratar Magajin Garin Daura kuma dan uwan sarkin Daura ne Alhaji Faruk Umar.

Yadda ‘yan bindiga suka sace surukin Buhari a Daura
Yadda ‘yan bindiga suka sace surukin Buhari a Daura
Source: UGC

KU KARANTA:Ku tuba zuwa ga Allah ko mu lalataku da Al-Qunuti – Izala ga masu garkuwa da mutane

Wani wanda lamarin ya auku a kan idonsa ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa, mutanen sun zo ne cikin motoci biyu Peugeot 406 da kuma Toyota hilux inda suka sauka daidai gidan Magajin Garin.

“ Sun taddashi gaban gidanshi dake Kwanar Agam yayinda suka tilasta mashi da karfi da yaji ya biyo su da misalin karfe 7 na maraice jim kadan bayan sallar Magariba.”

Wani shima wanda lamari ya faru akan idonsa, mai suna Mallam Muhammad wanda makwabcine ga Magajin Garin yace abin ya aukune yadda kasan wani wasan kwaikwayo.

“ Tare dashi mukayi sallar magariba. Bayan mu idar ya kama hanyarsa ta zuwa gida, idan ya isa gida ya kasance ya saba da zama a gaban gidanshi har sai bayan sallar isha’i kafin ya shiga gida.

“ Bugu da kari, a daidai lokacin da Magajin garin ke zaune a gaban gidan nashi sai muka ga ya amsa wayarsa ga alama wanda ya kirashi ce masa yayi gani tafe zuwa wurinka.

“ Yan mintuna kadan kwatsam sai ga wasu motoci sun bayyana a gaban gidanshi, suna tsayawa suka wuce zuwa ga Magajin garin suka tazgoshi zuwa daya daga cikin motocinsu. Mutanen dake tare dashi sun yinkuro domin cetonsa amma sai yan bindigar suka fara sakin albarushi don kada kowa ya matso kusa dasu.” Inji Mallam Muhammad.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Tags:
Online view pixel