Karancin lebarori daga kasashen waje zai kawo sauyin farashin abinci, inji Manoma

Karancin lebarori daga kasashen waje zai kawo sauyin farashin abinci, inji Manoma

-Akwai yiwuwar samun hauhawar farashin abinci saboda lebarori sunyi karanci a gona

-Matsalar tattalin arziki Najeriya shine ya haifar da wannan matsala, saboda hadiman basu ga wani bambamci ba tsakanin Naira da kudin da suke amfani dashi a kasashensu ba

Hasashe ya nuna cewa nan da watanni kadan farashin abinci zai hawa idan har ba’ayi wani abu ba akan magance matsalar lebarorin gona musamman a yankin kudu maso yammacin kasar nan, kamar yadda jaridar INDEPENDENT ta bayyana.

Bincike ya nuna cewa akasarin lebarorin sun fito ne daga kasashen Togo, Benin da Ghana, sun kasance yanzu basu zuwa saboda rashin darajar Naira a fanni tattalin arziki wanda idan suka zo abinda ake biyansu bai isarsu.

Karancin lebarori daga kasashen waje zai kawo sauyin farashin abinci, inji Manoma

Karancin lebarori daga kasashen waje zai kawo sauyin farashin abinci, inji Manoma
Source: UGC

KU KARANTA:Wuya: Halin da mayakan kungiyar Boko Haram suka shiga bayan sojoji sun tagayyara su

Manoma sun bayyana wannan lamari a matsayin abinda kan iya haifar da raguwar amfanin gona. Saboda baza su iya noma yawan abinda suke nomawa a dab a, duk a daliln rashin ma’aikatan da ke taimaka musu gashi kuma basu da tarikita.

Wasu daga cikin manoma da suka zanta da wakilinmu sun nuna damuwarsu akan darajar Naira wacce kullum ke kara raguwa a matsayin abinda ya haifar da wannan matsalar. Wannan dalilin shine yake hana lebarorin zuwa.

Sun sake cewa, akwai bukatar tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa saboda darajar Naira ta karu domin samun martaba da kima ko da kuwa ba nan kasar ba.

Wale Oyekoya wanda yake manomi ne kuma tsohon shugaban kungiyar kasuwancin a jihar Legas cewa yayi karancin lebarori a harkar noma yana haifar da hauhawar fasahin albarkatun gona.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel