Boko haram: Zamu taimaka idan har kuka nemi hakan wajen yaki da ‘yan ta’addan, kasar Ingila ta fadawa Najeriya

Boko haram: Zamu taimaka idan har kuka nemi hakan wajen yaki da ‘yan ta’addan, kasar Ingila ta fadawa Najeriya

-Kasar Ingila a shirye take da ta taimaki Najeriya domin ganin bayan kungiyar Boko haram

-Ko shakka babu zamu bada namu taimakon idan an nemi muyi hakan, zance daga bakin sakataren harkokin waje na Ingila

Sakataren harkokin waje na kasar Ingila Jeremy Hunt shine ya bayyanawa Najeriya cewa idan har suna bukatar wani taimako daga wajensu a shirye suke domin su bada.

Hunt yace ana gwabza rikici tsakanin sojin Najeriya da kuma kungiyar Boko haram a yankin arewa maso gabas na Najeriya wanda har yanzu yaki ci yaki cinyewa.

Boko haram: Zamu taimaka idan har kuka nemi hakan wajen yaki da ‘yan ta’addan, kasar Ingila ta fadawa Najeriya

Boko haram: Zamu taimaka idan har kuka nemi hakan wajen yaki da ‘yan ta’addan, kasar Ingila ta fadawa Najeriya
Source: UGC

KU KARANTA:JAMB za ta soke fiye da rabin sakamakon jarrabawa a wasu jihohin Najeriya

Yace “ wani bayani na sirri da yazo min” ya nuna cewa rashin jituwa tsakanin jami’ai da kuma ‘yan asalin wadannan yankin shike ke kara sanya rikicin na yin gaba a maimakon ace yana raguwa.

Bugu da kari, gwamnatin Burtaniya a shirye take da ta taimaka matukar an nemi yin hakan daga wajenta.

Gwamnatin kasar Burtaniya a shekarar 2017 ta sanar da wata yarjejiniyar horar da sojin Najeriya kan kudi £200m na tsawon shekara hudu daga 2018 zuwa 2022.

Hunt ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da ya ziyarce Maiduguri a wata ziyara da yakeyi kasashen Afrika domin karfafa alaka tsakanin kasashen Afrika da kuma kasar Ingila.

“ Nazo nan Maiduguri ne inda ke fama da rikicin Boko haram wanda yayi sanadiyar samar da yan gudun hijira kimamin mutum miliyan 2, a halin yanzu suna rayuwa a sassanin yan gudun hijira.” Hunt ya fadi.

“ A shirye muke domin taimakon sojin Najeriya wurin kawo karshen rikicin Boko haram. Bukata a nan shine kawai sai idan kun nemi taimakon kuma kun nuna sha’awa ba wai zamu shigo muku kasa ba tare da amincewarku ba.” Hunt ya sake jaddadawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel