Wuya: Halin da mayakan kungiyar Boko Haram suka shiga bayan sojoji sun tagayyara su

Wuya: Halin da mayakan kungiyar Boko Haram suka shiga bayan sojoji sun tagayyara su

Biyo bayan matsin lamba da mayakan kungiyar Boko Haram ke fuskanta a hannun dakarun sojin hadin guwuiwa na kasashen gefen tekun Chadi (MNJTF) da kuma dakarun soji na cikin gida, yanzu haka mayakan sun shiga matasanancin halin rashin abinci da makamai.

Matsanancin halin da mayakan kungiyar Boko Haram suka shiga ya tilasta su yin basaja wajen shiga gari domin neman abincin da zasu ci da kuma makaman da zasu yi amfani da su.

Sai dai, wasu daga cikin mayakan da basu yi basaja domin shiga gari ba, sun koma kai hare-hare a kan kananan kauyuka domin su kwashi abinci da dabbobin da zasu yi kalaci da su.

Mayakan sun shiga wannan matsanancin hali ne sakamakon tarwatsa su da lalata maboyar su da dakarun MNJTF da kuma dakarun sojin cikin gida karkashin atisayen Ofireshon lafiya dole suka yi a 'yan kwanakin baya bayan nan.

A kokarinsu na ganin cewar sun cigaba da kai hare-hare don kar a gane rauninsu, mayakan sun koma kai hare-hare a kan jama'a marasa karfi da kananun cibiyoyin sojoji. A daya daga cikin irin wadannan hare-haren ne dakarun soji na rundunar atisayen 'Forward Operation Base (FOB)' suka yi kacibus da mayakan na kungiyar Boko Haram a garin Damboa a ranar 27 ga watan Afrilu.

Wuya: Halin da mayakan kungiyar Boko Haram suka shiga bayan sojoji sun tagayyara su

Dakarun soji
Source: Twitter

Yayin fafatawar su, dakarun soji sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram da dama duk da su ma sun rasa wasu jami'ai kalilan, sannan an lalata musu wasu kayan aiki, wasu dakarun kuma sun samu raunuka daga harbin bindiga. Duk da tuni al'amura sun koma daidai a yankin, dakarun soji sun mamaye dukkan wata hanya da ragowar mayakan da suka gudu zasu iya amfani da ita domin samun tsira.

DUBA WANNAN: Bafarawa ya zayyana illolin da rashin tsaro ke yiwa tattalin arzikin Najeriya

Bayan samun wannan gagarumar nasara ne rundunar soji tayi kira ga jama'a da su yi watsi da duk wani labari dake nuna cewar mayakan Boko Haram sun kashe dakarun rundunar soji yayin fafatawar, rundunar ta ce masu tausayin 'yan ta'addar ne ke yada irin wadannan labarai.

Kazalika, rundunar tayi kira na musamman ga jama'a a kan su goyi bayan dakarun soji ta hanyar bayar da muhimman bayann da zasu taimaka wajen murkushe duk wani abu mai alaka da kungiyar Boko Haram.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel