Yadda yawon Buhari ke damalmala harkar tsaro a Najeriya - PDP

Yadda yawon Buhari ke damalmala harkar tsaro a Najeriya - PDP

An bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya katse ziyarsa da ya kai kasar Ingila ya dawo gida Najeriya domin ya mayar da hankali a kan harkokin kasar musamman batun tsaro.

Kola Ologbodiyan, Kakakin Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ne ya yi wannan jawabin a wata sanarwa da jaridar Sahara Reporters tayi karo da shi a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce: "Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), tana kallubalantar shugaba Muhammadu Buhari ya kawo karshen ziyarsa a kasar waje ya dawo gida ba tare da bata lokaci ba domin ya magance kallubalen tsaro da ake fama da shi a kasar.

Yadda yawon Buhari ke damalmala harkar tsaro a Najeriya - PDP

Yadda yawon Buhari ke damalmala harkar tsaro a Najeriya - PDP
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Bayan cin zabe a PDP, shugaban marasa rinjaye ya koma APC

"Jam'iyyar ta ce ba zai yiwu shugaban kasar ya yi watsi da aikinsa a matsayin babban kwamandan sojojin Najeriya ba bisa wasu dalilai da ba a bayyana ba yayin da 'yan bindiga, 'yan ta'ada da bata gari suke cin karensu ba babaka a kasar.

"Rashin mayar da hankali a kan ta'addanci ya bawa 'yan bindiga karin gwiwar cigaba da kaiwa al'umma farmaki a Borno, Zamfara, Yobe Adamawa, Gombe, Taraba, Kaduna Benue, Kogi da wasu jihohin Najeriya ciki har da jihar shugaban kasa wato Katsina.

"A yayin da shugaban kasa ke yawo a kasashen ketare, 'yan bindiga suna ta cin karensu ba babbaka a garuruwan Katsina inda suka kashe mutane da dama kuma suka sace basarake a Daura, Musa Umar surukin mai tsaron shugaban kasa. A wannan lokacin ne kuma wasu bata gari sukai kai hari wasu garuruwan Adamawa inda suka kashe a kalla mutane 26; an kuma kashe wasu a Borno, Taraba, Benue da Zamfara inda aka ce wasu 'yan bindiga sun kai hari Makarantar Sakandire ta Moriki inda suka sace wasu 'yan mata a makarantar.

"A yayin da gwamnatin Buhari tayi burus da batun tsaro a kasar, masu garkuwa da mutane sun mamaye manyan titinan mu inda suka sace 'yan kasa da dama da suke rike da su a daji a hanyoyin Kaduna-Abuja, Taraba-Katsina-Ala da wasu manyan tituna a kasar."

Sakon ya cigaba da cewa akwai zargin cewa zargin cewa 'yan bindigan da ke kai hari a wasu jihohi baki ne da jam'iyyar APC da dauko haya daga Nijar domin taimaka mata wurin tayar da hankula domin lashe zaben 2019.

Jam'iyyar ta PDP ta bukaci rundunar 'yan sanda ta gudanar da bincike a kan wannan zargin duba da cewa shugaban kasar ba shi da niyyar kawo karshen wannan bala'i.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel