Almundanar kudi: An gurfanar da manyan jami'an gwamnatin jihar Kwara hudu a gaban kuliya

Almundanar kudi: An gurfanar da manyan jami'an gwamnatin jihar Kwara hudu a gaban kuliya

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC reshen garin Illorin ta gurfanar da wasu jiga-jigan gwamnatin Jihar Kwara a gaban kuliya a ranar Alhamis 2 ga watan Mayu a gaban Mai shari'a Justice Babagana Ashigar na kotun tarayya da ke Ilorin bisa zarginsu da karkatar da kudaden gwamnati.

Wadanda aka gurfanar a kotun sun hada da Abubakar Ishiak, babban sakatare a jihar; Shina Mudasir Akorede, Dirketan Kudi da harkokin mulki; Rasaq Momonu, Mai kula da Kudade da asusun ajiyar kudi, da kuma Hafeez Yusuf, jami'i mai fitar da kudade.

Almundanar kudi: An gurfanar da manyan jami'an gwamnatin jihar Kwara hudu

Almundanar kudi: An gurfanar da manyan jami'an gwamnatin jihar Kwara hudu
Source: Depositphotos

Karar ta ce: "Abubakar Ishiak, babban sakataren gidan gwamnatin Kwara, Shina Mudasir Akorede, Direktan harkokin mulki da kudi, Rasaq Momonu, mai kula da kudade da asusun ajiya na gidan gwamnatin Kwara da Hafeez Yusuf a matsayin ka jami'in fitar da kudade kun sanya hannu an biya kudi N20,300,000 (Miliyan ashirin da dubu dari uku) ga wata kamfani guda daya mai suna Energy Multi-Trade Unique Interbiz Limited ta hannun shugaban kamfanin Jimoh Sarafadeen Kolade a ranar 14 ga watan Fabrairun 2019 1 Ilorin saboda wasu ayyuka da ya yiwa gwamnatin jihar Kwara sai sai wannan ya sabawa sashi na 1 (b) na doka da ya hana biyan kudi sama da Naira Miliyan 10 ga kamfanoni kuma akwai hukunci da doka ta tanadar a sashi na 16."

DUBA WANNAN: Bayan cin zabe a PDP, shugaban marasa rinjaye ya koma APC

Sai dai wadanda aka gurfanar a kotun sun amince da aikata laifin.

Hakan ya sa lauyan EFCC, Christopher Mschelia ya bukaci kotu ta sanya ranar da za a fara sauraron shari'a saboda a bayyana hujja a kansu.

"Muna rokon Alkali ya tsare wadanda ake zargin a gidan yari," inji Mschelia.

Sai dai lauya da ke kare wadanda aka gurfanar Abdulwahab Bamidele ya bukaci kotun ta bayar da belin su.

Alkalin kotun, Mai shari'a Ashigar ya hana belin inda ya bukaci a cigaba da tsare su a hannun hukumar EFCC.

An dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 8 ga watan Mayun 2019 domin zaman sauraron bayar da beli sannan kuma za a fara shari'a a ranar 6 ga watan Yulin 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel