JAMB za ta soke fiye da rabin sakamakon jarrabawa a wasu jihohin Najeriya

JAMB za ta soke fiye da rabin sakamakon jarrabawa a wasu jihohin Najeriya

Mai yiwuwa hukumar shirya jarrabawar shiga gaba da makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta soke fiye da rabin sakamon jarrabawar da aka yi a shekarar 2019 a wasu jihohin kasar nan, kamar yadda wani ma'aikacin hukumar ya shaida wa majiyar mu.

Jami'in, wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya ce JAMB za ta soke sakamakon jarrabawar ne saboda magudin da aka tafka yayin rubuta jarrabawar da aka yi tsakanin 11 zuwa 18 ga watan Afrilu.

Majiyar ta ce duk da an tafka magudi a kowanne bangare na Najeriya, lamarin ya fi muni a wasu jihohin. Ya ce: "iyayen yara da masu cibiyar rubuta jarrabawa sun taimaka wajen magudin da aka tafka yayin jarrabawar, lamarin ya matukar bawa hukumar JAMB mamaki."

Da yake karin bayani a kan jinkirin da ake fuskanta wajen samun sakin sakamakon jarrabawar, majiyar ta ce da 'yan Najeriya za su ga faifan bidiyo da na'urorin da aka saka a cibiyoyin rubuta JAMB 700 suka nada, da sun sha mamakin yadda aka tafka magudi yayin jarrabawar ba tare da shakka ko tsoro ba.

JAMB za ta soke fiye da rabin sakamakon jarrabawa a wasu jihohin Najeriya

JAMB za ta soke fiye da rabin sakamakon jarrabawa a wasu jihohin Najeriya
Source: Depositphotos

Ya ce hukumar JAMB za ta soke a kalla kaso 50% na sakamakon jarrabawar a wasu jihohin kasar na..

Jami'in ya cigaba da cewa, "ni ma na yi matukar girgiza da abinda na gani, yadda aka tafka magudi ba tare da tsoro ba duk da irin matakai na fasaha da hukumar JAMB ta dauka. Ban san kuma me zamu yi don magance magudin jarrabawa ba.

DUBA WANNAN: In da ranka: An samu wata macijiya mai ido uku (Hoto)

"Ina jin mutanen dake da hannu a cikin magudin da aka tafka basu dauka cewar na'urar nadar bidiyo da muka saka na yin aiki ba. Basu yarda cewar da gaske muke yi ba a kokarin mu na dakile magudin jarrabawa, domin da sun gaskata mu, ba zasu aikata abinda suka yi ba."

Kakakin hukumar JAMB, Fabian Benjamin, ya tabbatar da cewar an tafka mugun magudi yayin jarrabawar, ya ce hukumar ba zata nuna wariya ga wani yanki ba wajen daukan mataki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel