Ganduje ya sallami dukkan manyan sakatarorin ma'aikatun jihar Kano

Ganduje ya sallami dukkan manyan sakatarorin ma'aikatun jihar Kano

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya bayar da umurnin a sallami dukkan manyan sakatarorin ma'aikatun gwamnati a jiharsa daga aikinsu zuwa ranar Laraba 8 ga watan Mayun 2019.

A cikin wasikar da aka aike a ranar 2 ga watan Mayun 2019 mai dauke da sa hannun shugaban ma'aikatan jihar, Mohammed Awwal-Na'iya, gwamnan ya bukaci su mika aiki ga manyan direktocin ma'aikatunsu ko hukumominsu.

Gwamnan ya shawarci dukkan manyan sakatarorin da aka sallama da sauran direktoci da ke mataki na 16 ko 17 da ke sha'awar kujerar su mika takardun neman aikinsu da bayyanan karatunsu ga ofishin shugaban ma'aikata na jihar kafin karfe hudu na yammacin ranar 9 ga watan Mayun 2019.

Ganduje ya sallami dukkan manyan sakatarorin Kano

Ganduje ya sallami dukkan manyan sakatarorin Kano
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Bayan cin zabe a PDP, shugaban marasa rinjaye ya koma APC

Wasikar ta ce: "Kamar yadda ya ke a tsarin gwamnati mai ci yanzu na kawo sabbin tsare-tsare na inganta aiki da kawo sabbin jini a manyan mukamman gwamnatin jihar, gwamnatin ta bayar da umurnin sallamar dukkan manyan sakatarorin ta ba tare da bata lokaci ba.

"An bukaci su mika aiki ga manyan direktocin ma'aikatunsu ko hukumominsu zuwa ranar Laraba 8 ga watan Mayun 2018 kuma su garzaya zuwa ofishin shugaban ma'aikata domin sannin matakin gaba.

"Dukkan direktoci da ke mataki na 16 ko 17 da manyan sakatarorin da aka sauke daga mukamansu da ke sha'awar darewa kan kujerar su mika takardun karatunsu da aiki zuwa ga ofishin shugaban ma'aikata zuwa kafin karfe hudu na yammacin ranar Alhamis 9 ga watan Mayun 2019."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel