Yadda 'yan sanda suka dinga yiwa 'yan matan da suka kama fyade a Abuja

Yadda 'yan sanda suka dinga yiwa 'yan matan da suka kama fyade a Abuja

Wasu daga cikin matan da aka kama su a Abuja da zargin karuwwanci, a yau Alhamis dinnan su ka bayyana yadda wasu 'yan sandan Najeriya suka ci zarafin su a babban birnin tarayya Abuja

'Yan matan da su ka bayyana yadda abin ya faru, sun zargi jami'an 'yan sandan Utako dana Gwarimpa da ke Abuja, da yi musu fyade sannan kuma suka ci zarafin su.

Sun kuma bayyana cewa aan tilasta su akan sai sun amsa laifinsu a lokacin da aka gurfanar da su a gaban kotu ranar Litinin din da ta gabata.

'Yan matan sun ce an kama su a wurin casu da dare, inda aka kulle su a ofishin 'yan sanda, sannan aka dinga saka musu barkonon tsohuwa.

Yadda 'yan sanda suka dinga yiwa 'yan matan da suka kama fyade a Abuja

Yadda 'yan sanda suka dinga yiwa 'yan matan da suka kama fyade a Abuja
Source: Facebook

Wata a cikinsu ta bayyana cewa wani daga cikin jami'an 'yan sandan Utako da ake kira 'Yellow', ya buge ta da gindin bindiga, sannan ya dinga zabga mata bulala, har sai da ta ji ciwo a hannu da fuskarta.

Wata kuma wacce ta ce sun kamo ta a shagon sayar da kaya, ta ce jami'an 'yan sandan sunyi mata fyade saboda ba ta da kudin da za ta basu cin hanci.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari makarantar sakandare ta mata a jihar Zamfara

Matar ta ce jami'an 'yan sanda uku ne suka riketa inda na hudun kuma ya dinga amfani da ita ba tare da wata kariya ba.

Ta kara da cewa, wasu 'yan matan guda biyu suma haka 'yan sandan suka yi musu fyade a lokaci daya.

Ta ce: "Duka mu ukun haka suka fito damu daga cikin motar bayan sun gama yi mana fyade, saboda ba mu da kudin da za mu basu cin hanci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel