Wata mata ta maka tsohon mijinta da sabuwar amaryarsa kotu kan kiranta da suna karuwa

Wata mata ta maka tsohon mijinta da sabuwar amaryarsa kotu kan kiranta da suna karuwa

Wata mata mai shekara 21 a duniya, Rahina Muhammad a ranar Alhamis ta maka tsohon mijinta, Sani Hassan da sabuwar amaryarsa Hauwa, a gaban kotun shari’a da ke zauna a Magajin Gari, Kaduna, kan kiranta da sunan karuwa.

Mai karar, wacce zauna a hanyar Zaria da ke Kaduna, ta fada ma kotu cewa Hassan ya ci gaba da kiranta a wayar tarho, don ya zage ta da kuma kiranta da sunayen banza.

“A duk lokacin da ya kirani, sai yayi ta tsine mun, cewa babu namijin da zai aure ni. Na sha kai karansa gaban magabatanmu domin su gargade sa akan furucinsa amma abun yaci tura,” inji ta.

Ta kara da cewa har ya kai amaryar Sani ma na kiranta ta zage ta.

Wata mata ta maka tsohon mijinta da sabuwar amaryarsa kotu kan kiranta da suna karuwa

Wata mata ta maka tsohon mijinta da sabuwar amaryarsa kotu kan kiranta da suna karuwa
Source: Twitter

Ta roki kotu da ta sanya baki a lamarin sannan ta bi mata hakkinta.

Da suke kare kansu, wadanda ake karan guda biyu sun karyata ikirarin, cewa ba gaskiya bane.

Alkalin Malam Dahiru Lawal, bayan sauraron bangarorin biyu, ya nemi mai karar ya gabatar da shaidu.

KU KARANTA KUMA: Kasar UAE tayi sabbin dokokin hukunta mazan dake yiwa mata kallon kurilla

Alkalin ya tsare su a gidan yari, zuwa lokacin bayar da belinsu. Ya dage sauraron shari’an Zuwa ranar 9 ga watan Mayu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel