Gwamnati za ta yiwa Makarantun Almajirai tsarki a jihar Kano

Gwamnati za ta yiwa Makarantun Almajirai tsarki a jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano ta kudiri aniya tare da daura damarar fuskantar kalubalen ta'ammali da miyagun kwayoyi da kuma barace-barace a kan titunan ta kamar yadda Muhiyi Magaji Rimingado ya bayyana, shugaban gidauniyar hadin kan gwamnati OGP.

Rimingado wanda ya kasance jagoran cibiyar karbar korafe-korafen al'umma da yaki da rashawa, ya ce tuni gwamnatin jihar ta dukufa wajen gudanar da bincike domin gano bakin zaren na kawo karshen ta'ammali da miyagun kwayoyi da kuma barace-barace a Kanon Dabo.

Gwamnan jihar Kano; Abdullahi Ganduje

Gwamnan jihar Kano; Abdullahi Ganduje
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jagoran cibiyar hana yiwa tattalin arziki ta'annati ya bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa yayin ganawar sa da manema labarai cikin birnin Kano a ranar Alhamis.

Kazalika cikin sanarwar sa, ya ce gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar kungiyar zamantakewar al'umma, ta daura damarar gudanar da bincike domin kawo managarcin tsarki a harkokin makarantun almajiranci.

Alhaji Magaji ya yi kira ga kafafofin sadarwa da yada rahotanni a kan wayar da kan al'umma dangane da muhimmancin wannan muhimmin aiki da gwamnatin jihar Kano ta kudirci aiwatar wa domin inganta ci gaban jihar da kuma kasa baki daya.

KARANTA KUMA: Shekarau ya nemi 'yan siyasa su hada kai da Buhari domin ci gaban kasa

Ya kara da cewa ba bu al'ummar da za ta taka mataki na ci gaba matukar almajarai da masu yawon barace-barace na kai komo a tsakanin al'umma da hakan ya ke haifar da aukuwar miyagun ababe na sharri.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel