Jarumta: FRSC ta yiwa wasu jami'anta 2 karin girma

Jarumta: FRSC ta yiwa wasu jami'anta 2 karin girma

Hukumar Kiyaye Hadura na Tarayya FRSC) ta karrama wasu jami'anta biyu da ke aiki a jihar Abia a ranar Juma'a inda aka yi musu karin girma saboda jarumta da juriya da suka nuna wurin aiki.

Kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito masu tsaron matar Kakakin Majalisar jihar Abia ne suka harbi jami'an biyu - Anya Nnachi da Chukwuemeka Ogbuja yayin da suke kokarin tabbatar doka da oda a titin Abia zuwa Fatakwal.

Lamarin ya afku ne a watan Yulin 2017.

Shugaban hukumar ya yankin Enugu, Osadeba Osadebanwen ne ya nada wa jami'an sabon mukamin su a garin Enugu inda ya ce anyi musu karin girman ne saboda jarumta da su kayi duk da harin da aka kai musu.

DUBA WANNAN: Tsallake rijiya da baya: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan Zainab Aliyu

Jarumta: FRSC ta yiwa wasu jami'anta 2 karin girma

Jarumta: FRSC ta yiwa wasu jami'anta 2 karin girma
Source: Depositphotos

Mr Osadebanwen ya kuma yabawa Corp Marshal Boboye Oyeyemi saboda daukan dawainiyar kudin asibitin jami'an biyu inda ya ce abinda ya aikata abin koyi ne ga sauran jami'an hukumar.

A jawabinsa, Kwamandan Hukumar na Jihar Abia, Menshak Jatau ya yiwa Allah godiya saboda kiyaye rayukan jami'an biyu kuma ya yabawa shugaban hukumar saboda karbar afuwar gwamnatin jihar Abia bisa afkuwar lamarin.

Kazalika, Kwamandan FRSC na jihar Enugu, Kalu Ogbonnaya ya yiwa jami'an biyu jinjina saboda jajircewa da su kayi a kan aikinsu duk da afkuwar lamarin.

Daya daga cikin wadanda aka yiwa karin girman, Mr Ogbuja ya yiwa mahukuntar FRSC godiya musamman shugabansu, Boboye Oyeyemi saboda karamcin da ya yi musu inda ya ce hakan zai kara musu kwarin gwiwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel