Malamin addinin Islama ya bayyana kalar musulmin da ke kashe Jama'a

Malamin addinin Islama ya bayyana kalar musulmin da ke kashe Jama'a

Fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Muyideen Bello ya ce mutanen da ke kashe mutane da sunnan Allah ba musulmi bane na gaskiya.

Bello ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke gabatar da kasidar maraba da watan Ramadan da gidan talabijin na tarayya, NTA reshen garin Oshogbo ta shirya a ranar Alhamis.

A yayin da ya ke kushe wadanda ke amfani da sunan Allah domin aikata zalunci, Bello ya ce Allah ba ya bukatar kowa ya kashe wani da sunnan kare sunnan sa.

"Ba za mu iya dawo da kimar dan adam ba ta hanyar kashe mutanen da basu ji basu gani ba.

"Ya zama dole mu guji aikata duk wani abu da zai sanya a rika yi mana kallon masu tsatsauran ra'ayi tunda dama bamu da irin wannan ra'ayin.

"Duk wanda ya kashe wani kuma yana kiran sunan Allah ba musulmi bane kuma wuta zai shiga a gobe kiyama," inji Bello.

Malamin addinin Islama ya bayyana kalar musulmin da ke kashe Jama'a

Malamin addinin Islama ya bayyana kalar musulmin da ke kashe Jama'a
Source: Twitter

A yayin da ya ke bayyana addinin musulunci a matsayin addinin zaman lafiya, shararen mai wa'azin ya bukaci al'ummar musulmi su tabbatar da cewa sun zauna lafiya da juna a garuruwansu duk da banbance-banbancen addini da ke tsakanin al'umma.

DUBA WANNAN: Ganduje ya yi alkawarin fara biyan ma'aikatan Kano sabuwar albashi

Ya kara da cewa addinin musulunci mika wuya ne ga Allah kuma abinda ake bukata ga musulmi shine suyi imani da Allah kuma su bauta masa sannan suyi imani shine ke bayarwa da karba.

A yayin da ya ke kira ga kungiyoyin musulmi su zauna lafiya da junansu, Bello ya ce ba daidai bane musulmi su tilastawa wadanda ba musulmi ba shiga addinin musulunci.

Bello ya ce sai akwai zaman lafiya za a samu cigaba kuma ya shawarci dukkan muminai su rika yiwa juna kallon 'yan uwa kuma su bari Allah ya bayyana addinin da za ta zama karbabiya gareshi a ranar kiyama.

A jawabinsa, Gwamna Gboyega Oyetola ya ce zaman lafiya tsakanin addinai itace ginshikin walwala da cigaban tattalin arziki a kowane gari.

Oyetola, wanda mataimakin shugaban ma'aikatan jiharsa, Alhaji Abdullahi Binuyo ya wakilta ya bukaci musulmi a Najeriya su cigaba da yada zaman lafiya su kuma guji abinda zai tayar da hankulan al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel