Bayan cin zabe a PDP, shugaban marasa rinjaye ya koma APC

Bayan cin zabe a PDP, shugaban marasa rinjaye ya koma APC

Shugaban marasa rinjaye na majalisar jihar Ogun, Mr Olawale Alausa ya sauya sauka sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, (PDP) zuwa jam'iyyar All Progressives Congress, (APC).

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Ijebu-Ode ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar ne a cikin wata wasika da ya aike a ranar 23 ga watan Afrilu da Kakakin majalisa, Mr Suraj Adekunbi ya karanto yayin zaman majalisar a ranar Alhamis a garin Abeokuta.

Dan majalisar ya ce da yanke shawarar sauya shekar ne bayan ya yi shawara da al'ummar mazabarsa da magoya bayansa.

Bayan cin zabe a PDP, shugaban marasa rinjaye ya koma APC
Bayan cin zabe a PDP, shugaban marasa rinjaye ya koma APC
Source: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu Yanzu: Mahukunta a kasar Saudiyya sun sako Ibrahim Abubakar

"Ina son in sanar da ofishin ka mai martaba cewa na koma jam'iyyar APC bayan nayi shawara da al'ummar mazaba ta," inji shi.

A bangarensa, Kakakin Majalisar ya yi masa fatan alheri a sabuwar jam'iyyar da ya shiga.

"Muna yi maka maraba da shigowa mataki na gaba (next level)," inji shi.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa cikin mambobin majalisar jihar 26, guda 18 'yan jam'iyyar APC ne, uku 'yan jam'iyyar APM, uku 'yan ADC sannan guda biyu 'yan jam'iyyar PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel