Shekarau ya nemi 'yan siyasa su hada kai da Buhari domin ci gaban kasa

Shekarau ya nemi 'yan siyasa su hada kai da Buhari domin ci gaban kasa

Tsohon gwamnan jihar Kano Mallam Ibrahim Shekarau, ya shawarci 'yan siyasa da su ka sha kasa a yayin babban zaben kasa na bana da su hada gwiwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin gina kyakkyawan tubali na ci gaban kasa.

Shekarau ya yi furucin hakan ne yayin halartar taron bikin kaddamar da wani sabon littafi da aka wallafa kan kwazo da nasarorin gwamnatin shugaban kasa Buhari tsawon shekaru hudu da ta shafe a bisa karagar mulki.

Shekarau ya nemi 'yan siyasa su hada kai da Buhari domin ci gaban kasa

Shekarau ya nemi 'yan siyasa su hada kai da Buhari domin ci gaban kasa
Source: Depositphotos

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyar wayar da kai akan managarcin jagoranci, zaman lafiya da kuma ci gaban kasa ta AGLPD, ita ce ta daukin nauyin gudanar da wannan taro da aka gudanar a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayun 2019.

Shekarau wanda ya kasance tsohon shugaban kungiyar yayin amintuwa da cewar kasar Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubalai daban-daban, ya ce dole gishirin zaman duniya ya na kunshe da kalubalai.

A sanadiyar haka tsohon gwamnan na jihar Kano ya ke cewa, ba bu wani mamaki dangane da kalubalai da shugaban kasa Buhari ke fuskanta yayin rike akalar jagoranci duba da nasarori da gwamnatin sa ta samu tsawon shekarun da ya shafe a bisa karagar mulki.

KARANTA KUMA: Rashin tsaro: Majalisar Wakilai ta nemi Buhari ya bayyana a gaban ta

Yayin karin haske da cewa rayuwa na tattare da tufka da warwarar matsaloli, Shekarau ya ce gwamnatin shugaban kasa Buhari ba za ta gushe ba wajen ci gaba da inganta jin dadin al'ummar kasar nan.

Sabon zababben sanatan shiyyar Kano ta Tsakiya ya lura cewa, akwai wasu Ministoci cikin majalisar shugaba Buhari da su gaza ta fuskar sauke nauyin da rataya a wuyan su, ya ce hakan ba zai sanya a kauracewa yabawa tsayuwar daka ta shugaban kasa Buhari ba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel