Rashin tsaro: Majalisar Wakilai ta nemi Buhari ya bayyana a gaban ta

Rashin tsaro: Majalisar Wakilai ta nemi Buhari ya bayyana a gaban ta

Majalisar wakilai ta Najeriya a ranar Alhamis, ta sake gayyatar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya hallara a farfajiyar zauren ta domin bayyana mata yadda gwamnatin sa ke riko da al'amura na rashin tsaro da suka addabi kasar nan.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, majalisar wakilai na neman jin ta bakin shugaban kasa Buhari kan yadda gwamnatin sa ke tafiyar da al'amurran kawo karshen kalubalai na rashin tsaro da suka zamto sarkakiya a fadin Najeriya.

Wannan ita ce gayyata ta biyu cikin makonni uku da majalisar ta shigar na neman shugaban kasa Buhari ya hallara gaban ta domin samun karin haske kan babban kalubale na rashin tsaro da ya yiwa kasar nan dabaibayi.

Majalisar yayin zaman ta na ranar 11 ga watan Afrilun 2019, ta shigar da wani kudiri na tursasa shugaban kasa Buhari akan bayyana yadda gwamnatin sa ke tafiyar da al'amurran tsaro tare da gindaya wa'adin kwanaki biyu kacal a kansa.

Kazalika majalisar yayin zaman ta na ranar Talatar da ta gabata, ta nemi shugaba Buhari ya hallara gaban biyo bayan rincabewar al'amurran tsaro a mahaifar sa ta jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel