Muna da tabbacin nasarar Atiku da Mohammed a kotun zabe – Tawagar lauyoyin PDP

Muna da tabbacin nasarar Atiku da Mohammed a kotun zabe – Tawagar lauyoyin PDP

- Christ Uche (SAN) lauya Atiku Abubakar da PDP a kotun zaben shugaban kasa, ya nuna yakini akan nasarar wadanda yake karewa a kotu

- Babban lauyan wanda har ila yau shi ke kare zababen gwamnan jihar Bauchi yace zai yi nasara a kotun zaben gwamna

- Uche ya kuma kalubalanci shugaba Buhari da APC akan zargin kin warware wasu lamura da aka gabatar a karar da Atiku ya shigar

Christ Uche (SAN) wanda shine jagoran lauyoyin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar a kotun zaben shugaban kasa, da zababben gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed a kotun zaben gwamna da ke zama a jihar Bauchi ya nuna yakini akan nasarar wadanda yake karewa a kotu.

Atiku da jam’iyyarsa suna kalubalantar sakamakon zabe cewa anyi magudi sosai, sannan an take dokar zaben.

A takardar karan, Atiku da PDP sun nemi kotun zaben ta kaddamar dashi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Muna da tabbacin nasarar Atiku da Mohammed a kotun zabe – Tawagar lauyoyin PDP

Muna da tabbacin nasarar Atiku da Mohammed a kotun zabe – Tawagar lauyoyin PDP
Source: UGC

Sun kuma bukaci kotun zaben da ta soke zaben sannan tayi umurnin sake Sabon zabe wanda yayi daidai da koyarwar dokar zabe.

KU KARANTA KUMA: Jirgin makarantar koyon tuki ya yi saukar bazata a Ilorin

A cewar jaridar The Nation, babban lauyan yace dukkanin wadanda ake kara a sharian Atiku duk sun gabatar da martaninsu.

Uche ya kuma kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam'iyyar APC akan zargin kin warware wasu lamura da aka gabatar a karar da Atiku ya shigar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel