Osinbajo na jagorantar zaman majalisar zantarwa

Osinbajo na jagorantar zaman majalisar zantarwa

Mun samu cewa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo na jagorantar zaman majalisar zantarwa na kowane mako da aka saba bisa al'ada a dakin taro na Council Chambers da ke fadar Villa a babban birnin kasar nan na tarayya.

An fara gudanar da zaman majalisar da misalin karfe 4.00 na Yammacin Alhamis yayin da aka dage zaman da ya kamata ya gudana tun karfe 10.00 na safiya.

Osinbajo na jagorantar zaman majalisar zantarwa

Osinbajo na jagorantar zaman majalisar zantarwa
Source: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa, ba bu masaniyar dalilin da ya haifar da tsaikon zaman na manyan kasa, illa iyaka ana zargin an samu jinkiri domin bai wa mataimakin shugaban kasa isashen lokaci na dawowa daga tafiyar sa da ya kai ziyara jihar Legas.

Farfesa Osinbajo na ci gaba da wakilcin rike akalar jagorancin kasar nan yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari a makon da ya gabata ya kai ziyarar kwanaki goma kasar Birtaniya.

Shugaban kasa Buhari ya fice daga Najeriya a ranar Alhamis ta makon da ya gabata bayan kaddamar da wasu manyan ayyuka a birnin Maiduguri wanda gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin gwamna Kashim Shettima ta aiwatar.

A yayin da ake kyautata zaton daidaiton al'amurra kamar yadda aka kudirta, ana sa ran dawowar shugaban kasa Buhari cikin karshen wannan mako.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel