Yanzu yanzu: Kungiyar Biafra ta sanya ranar 30 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu

Yanzu yanzu: Kungiyar Biafra ta sanya ranar 30 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu

-Yankin kasar Igbo za suyi hutu ranar 30 ga watn Mayu

-Har yanzu muna nan kan bakarmu, inji kungiyar tawaye ta Biafra

Kungiyar Biafra ta sanya ranar 30 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu ga magoya bayanta da duk ilahirin yankin kasar Igbo domin tunawa da mazan jiya na yankin.

Kungiyar ta roki mabiyan addinai daban daban na kasar da su sanya yan uwan nasu cikin addu’a saboda a ranar 29 ga watan Mayu ne aka kashe mutanen nasu a wasu shekaru da suka shude.

Yanzu yanzu: Kungiyar Biafra ta sanya ranar 30 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu

Yanzu yanzu: Kungiyar Biafra ta sanya ranar 30 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu
Source: UGC

KU KARANTA:Gwamnatin Kebbi bata da matsaya akan biyan mafi karancin albashin N30,000

A wani zance da ya fito daga bakin sakataren labarai na kungiyar, Emma Powerful, wannan ranar ta kasance ranar tunawa da ta’addancin Boko haram da kuma ‘yan bindiga masu satar shanu.

Ya sake cewa, babu zirga-zirga a wannan ranar ko a kafa ko bisa ababen hawa. Kowa zai kasance a gidansa ne tsawon wannan ranar a yankin Biafra.

Wuraren bauta kamar coci-coci da masallatai za’a budesu a daren 29 ga watan Mayu domin gudanar da addu’o’i ga wadanda suka rasa rayuwarsu a rana makamanciyar wannan.

“ Dukkanin magoya bayan kungiyarmu dake fadin kasar nan zasu fito kan tituna domin jimami da kuma cigaba da nuna kudurin da muke kai. Zamu mika kokenmu a rubuce zuwa ofishin majalisar dinkin duniya domin a sama mana mafita.” Inji sakataren.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel