EFCC ta gurfanar da wani mutum da ya kashe fiye da miliyan 200 da aka tura asusun sa bisa kuskure

EFCC ta gurfanar da wani mutum da ya kashe fiye da miliyan 200 da aka tura asusun sa bisa kuskure

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta gurfanar da Mista James Olaoluwaniyi, kwastoman bankin Sterling a kan yin amfani da wasu kudi $59,220 da aka tura asusun sa bisa kuskure.

Sai dai, Olaoluwaniyi ya shigar da karar hukumar EFCC bisa zargin ta da tsare shi ba bisa ka'ida ba ba tare da neman a biya shi diyya ta N50,000.

A cikin takardar karar da ya shigar ta hannun lauyansa, Olaoluwaniyi ya roki kotun ta tilasta hukumar EFCC da jami'anta sakin sa ba tare da wani bata lokaci ba da kuma tsawatar masu a kan sake kama shi a nan gaba.

Ya shaida wa kotun cewar bai aikata wani mugun laifi ba da ya bawa hukumar EFCC damar tsare shi ba.

Sai dai, hukumar EFCC, a nata bangaren, ta shaida wa kotun cewar ta samu takardar korafi a ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 2018, a kan yadda Olaoluwaniyi ya yi amfani da $59,220 da aka tura bisa asusun sa bisa kuskure.

EFCC ta gurfanar da wani mutum da ya kashe fiye da miliyan 200 da aka tura asusun sa bisa kuskure

Jami'an EFCC
Source: Depositphotos

EFCC ta kara da cewa, Olaoluwaniyi ya amsa cewar ya yi amfani da kudin, amma ya ce ya aikata hakan ne saboda yana tsammanin wani abokin kasuwancinsa zai turo masa da wasu kudi ta cikin asusun da aka yi kuskuren tura masa kudin.

Hukumar ta kara da cewa an sanar da Olaoluwaniyi kuskuren da aka samu na aika masa kudin, amma a lokacin tuni ya kashe $39,554 daga cikin kudin duk da ya san cewar ba kudin da yake tsammani daga abokin kasuwancinsa ba ne.

DUBA WANNAN: Tsohon gwamnan PDP ya garzaya kotu da bukatar neman a raba auren su da matar sa

A cewar EFCC, bankin ya yi nasarar janye $19,666 daga cikin kudin, sannan Olaoluwaniyi ya mayar da $10,000, lamarin da ya mayar da kudin da ake nema a hannun sa zuwa $29,000.

Sannan ta kara da cewa kin biyan ragowar kudin da ake bin sa ne ya sa hukumar ta kama shi bayan ta karbi korafi daga bankin da kuma kamfanin dake da mallakin kudin.

EFCC ta kara da cewa bata tsare Olaoluwaniyi ba sai bayan da ya karya dukkan sharudan da ta bayar da shi beli a kan su.

Kazalika, ta bayyana cewar ta gurfanar da shi a gaban wata kotun tarayya dake Legas bisa tuhumar sa da aikata laifin sata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel