Dubi yadda aka shirya zaben kananan hukumomin Zamfara

Dubi yadda aka shirya zaben kananan hukumomin Zamfara

Idan ba ku manta ba a cikin ‘yan kwanakin nan ne aka ji cewa jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ce ta lashe kaf kananan hukumomin jihar Zamfara a zaben da ya gabata mako guda da ya wuce.

Sai dai yanzu mun samu karin bayani game da wannan zabe da aka yi Ranar 27 ga Watan Afrilun jiya, inda ake tunanin cewa zaben da aka yi bai da sahihanci a dalilin zargin murdiyar da aka tafka a kananan hukomin da ke fadin Jihar.

Wani bidiyo da wani mai bibiyar harkar zabe a Najeriya ya saka a kafofin yada labarai, ya nuna yadda aka tafka magudi na inna-naha a zaben da aka yi a Zamfara. ‘Yan takarar APC ne dai su kayi nasara a duka kananan hukumomi 14 na jihar.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ta doke PDP ta lashe zaben Zamfara

A wannan bidiyo da yake yawo yanzu a kafafen sadarwa, an ga wasu Bayin Allah ne cikin wani daki su na dangwala takardun zabe yayin da su ke surutunsu. Babu dai wata alama da ke nuna cewa jama’an Gari ne su ke kada kuri’ar su.

Dr. Mazi Chima Amadi wanda shi ne ya fitar da wannan bidiyo ya koka a kan yadda jihohi su ke gudanar da zaben bogi wajen nada shugabannin kananan hukumomi, kamar yadda yake ikirarin cewa an gani a wannan rumfar zabe a Zamfara.

Shi dai shugaban hukumar zabe na jihar Zamfara mai zaman kan-ta, Alhaji Muhammed Garba, ya bayyana cewa an yi zabe ne na gaskiya kuma na ke-ke-da-ke-ke, ba tare da an yi wata murdiya ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel