Surukin Dogarin Buhari: 'Yan Sanda sun yi alkawarin bayar da miliyan biyar ga wanda ya kawo labari

Surukin Dogarin Buhari: 'Yan Sanda sun yi alkawarin bayar da miliyan biyar ga wanda ya kawo labari

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta jihar Katsina ta ta yi alkawarin bayar da naira miliyan biyar ga duk mutumin da ya bayar da labari ko ya ke da masaniya da inda barayin suka sace Alhaji Musa Umar

Hakan ya zo ne bayan da wasu mutane guda hudu da ba a san daga ina suke ba suka je har gidansa a Daura suka yi awon gaba dashi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Gambo Isa, ya bayar da sanarwa cewa za a bayar da ladan ne saboda taimakawa hukumar 'yan sanda da bayanai akan barayin da suka sace hakimin, kuma hakan shine zai bai wa 'yan sandan damar ceto shi daga hannun barayin.

Surukin Dogarin Buhari: 'Yan Sanda sun yi alkawarin bayar da miliyan biyar ga wanda ya kawo labari

Surukin Dogarin Buhari: 'Yan Sanda sun yi alkawarin bayar da miliyan biyar ga wanda ya kawo labari
Source: Facebook

Kakakin rundunar ya bayyanawa manema labarai cewa, bayan sun samu labarin barayin sun sace hakimin, sun yi gaggawar bin su inda har suka yi musayar wuta a tsakanin su.

Da aka tambayi kakakin rundunar 'yan sandan ko barayin sun kira sun nemi a biya kudin fansa, ya bayyana cewa "A halin yanzu bazan iya cewa komai ba saboda tsaro."

Rahotanni sun nuna cewa Alhaji Umar Musa shi ne magajin garin Daura, kuma shine suruki ga babban dogarin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutaane sun bayyana dalilan da yasa suke satar mutane a kasar nan

Hakan na zuwa ne a yanzu da ake fama da matsalar tsaro a yankunan jihar Katsina, Zamfara, Kaduna da wasu yankuna na babban birnin tarayya Abuja.

Ko a jiya Laraba majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton cewa an yi jana'izar mutane goma sha hudu, a jihar Katsina wadanda suka mutu sanadiyyar wani mummunan hari da 'yan bindiga suka kai karamar hukumar Safana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel