Tsohuwar matar tsohon gwamnan PDP ta roki kotu ta karbi dan suka haifa ta damka mata

Tsohuwar matar tsohon gwamnan PDP ta roki kotu ta karbi dan suka haifa ta damka mata

A ranar Alhamis ne uwargida Clara Chime, tsohuwar matar tsohon gwamnan jihar Enugu, Sullivan Chime, ta bayyana a gaban wata kotun tarayya dake zamanta a yankin Apo a Abuja tare da rokon kotun a kan ta karbi dan da suka haifa da tsohon gwamnan domin ta cigaba da rikon sa.

Da take mayar da martani a kan bukatar da tsohon mijinta ya gabatar na neman a raba aurensu, uwargida Clara ta bayyana cewar a shirye take ta amince da hakan amma fa idan za a bata rikon dan da suka haifa da kuma biyanta N500,000 duk wata domin kula wa da yaron.

Clara ta shaida wa kotun cewar yaron baya samun kula wa sosai a gidan mahaifinsa sannan da kyar ake bari ta ganshi na tsawon sa'a biyar a kowanne wata, hakan ma sai a gaban dumbin jami'an tsaro.

Lauyar dake kare uwargida Clara ta shaida wa kotun cewar ko a baya, sau biyu tsohuwar matar gwamnan na rubuta takardar neman kotu ta karba mata yaron daga hannun tsohon gwamnan domin ta cigaba da rikon shi.

Tsohuwar matar tsohon gwamnan PDP ta maka shi a kotu

Tsohon gwamna Sullivan Chime
Source: Depositphotos

Da lauyan tsohon gwamnan ya tambayi Clara ko tana da wani hoto da zata iya nuna wa kotu a matsayin shaidar ta a kan abinda ta fada, sai ta ce jami'an tsaron tsohon gwamnan ba sa bari ta dauki hoto duk lokacin da ta ziyarci yaron.

DUBA WANNAN: Awon gaba: Yadda ake yiwa masu tafiya Saudiyya cushen kaya a filin jirgin Mallam Aminu Kano

Kazalika, Clara ta shaida wa kotun cewar ta samu kanta a cikin matsanancin halin damuwa sakamakon auren tsohon gwamnan, saboda tunda suka yi aure, tsawon shekara 11, a ranar amarcinta ne kawai gwamnan ya taba kusantar ta, ta ce tun bayan wannan lokacin bai kara ko taba jikinta ba.

Bayan sauraren kowanne bangare, alkaliyar kotun, Jastis Angela Otaluka, ta tsayar da ranar 10 ga watan Yuni domin cigaba da sauraron karar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel