Da Duminsa: ‘Yansanda sun Kama Mutanen da ake zargi da Yin Garkuwa da Surukin Dogarin Buhari!

Da Duminsa: ‘Yansanda sun Kama Mutanen da ake zargi da Yin Garkuwa da Surukin Dogarin Buhari!

‘Yansanda a jihar Katsina a yau Alhamis sunce an kama mutanen da ake zargi da hannu wurin yin garkuwa da surukin dogarin shugaban kasa muhammadu Buhari, kamar yadda kafar watsa labarai ta Channel ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar ‘yansanda ta jihar Katsina, Gambo Isah, a cikin wani bayani yace an sace Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Uba ranar Larba da marece a gidansa.

Ya kara da cewa masu garkuwa da mutanen wadanda yawan su yakai mutum shidda sun afka gidan ne a cikin wata mota kirar Peugeot 405 da bata da lamba, mai fenti bulu, sun yi harbe-harbe cikin iska, kuma suka sace shi.

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun karyata batun sace dalibai a makarantar mata na Zamfara

Kwamishinan ‘yansandan jihar da kungiyar ‘yansanda masu sintiri sun isa wurin da abun ya faru inda suka kama wasu daga cikin mutanen da ake zargi.

Harsashi ya samu daya daga cikin jami’an ‘yansandan a lokacin musayar wuta da masu garkuwa da mutanen.

Yace: “Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Sanusi Buba, tare da kungiyar ‘yansandan sintirin sun isa wurin da abun ya faru.

“Kungiyoyin ‘yansandan sintiri dake ofishin ‘yansanda na Yankin Kusada a jihar Katsina sun tare barayin kuma suka yi musayar wuta da su wanda a sanadiyyar hakan ne wani Sifetan ‘yansanda Muntari Maikudi dake aiki a ofishin na yankin Kusada ya samu raunin harbin harsashi inda aka garzaya da shi zuwa assibitin gwamnatin tarayya (FMC) dake garin Katsina don karbar magani.

“Tuni dai aka aika da Rundanar Kai Harin Dabaru ta Babban Sifetan ‘Yansanda, da kungiyoyin ‘yansandan yakar masu fashi da makami, da sassan dake kula da ayyukan ta’addanci, don ceto wanda aka sace a raye ba tare da wani abu ya same shi ba don mika shi ga iyalin shi.”

Rundunar ‘yansandan ta roki jama’a da su rika taimaka ma jami’an tsaro da muhimman bayanan tsaro a kodayaushe, dangane da ayukkan ‘yan fashi. Rundunar ta kara da cewa ita da sauran jami’an tsaro tsaye suke kyam don tabbatar da an kawo karshen ayukkan ‘yan fashin.

Basaraken gargajiyar da aka sace, wanda yake mahaifi ne ga Fatima Musa, matar Kanar Mohammed Abubakar, dogarin Shugaban Kasa Buhari, tsohon konturolan hukumar kwastom ne, kuma babban dan kasuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel