Hukumar INEC ba ta da hurumin rike min takardun shaidar samun nasarar zabe - Okorocha

Hukumar INEC ba ta da hurumin rike min takardun shaidar samun nasarar zabe - Okorocha

Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, ya ce hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, ba ta da ikon ci gaba da rike takardun sa na shaidar samun nasarar zabe.

Okorocha ya kasance dan takarar kujerar sanatan shiyyar Imo ta Yamma yayin babban zaben kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

Hukumar INEC ba ta da hurumin rike min takardun shaidar samun nasarar zabe - Okorocha

Hukumar INEC ba ta da hurumin rike min takardun shaidar samun nasarar zabe - Okorocha
Source: Twitter

Cikin korafin da ya gabatar a ranar Talatar da ta gabata, Gwamna Rochas ya bayyana takaicin sa dangane da yadda hukumar INEC ke ci gaba da rike takardun sa na shaidar cin zabe bayan tuni aka yi shellar nasarar sa ta lashe zaben da aka gudanar.

Sai dai kawowa yanzu hukumar INEC ta hau kujerar naki wajen mallakawa Okorocha takardun shaidar nasarar cin zabe a yayin da ta ke ci gaba da ikirarin cewa an yi shellar nasarar cikin yanayi na tursasawa.

Gwamnan ya ce a bisa tanadin kayyadewar dokokin zabe a kasar nan, hukumar INEC ba da ta uzuri na ci gaba da rike takardar sa ta shaidar nasarar lashen zaben kujerar Sanatan shiyyar Imo ta Yamma.

KARANTA KUMA: Gwamnatin mu ta shirya biyan N30,000 mafi karancin albashin ma'aikata a Kano - Ganduje

Yayin kafa hujja da sashe na 285 sakin layi na farko cikin kundin tsarin mulkin kasar nan, Okorocha ya ce duk wata takaddama bayan shellanta sakamakon zabe na karkatuwa tare da rataya a wuyan kotun daukaka karar zabe da aka tanada.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel