Rashin tsaro: Shehu Sani yace ba zai yi shiru yayin da ake kashe mutane ba

Rashin tsaro: Shehu Sani yace ba zai yi shiru yayin da ake kashe mutane ba

Sanatan da ke wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, Kwamared Shehu Sani, ya bayyana su kayi ta da wani Sanatan jihar Katsina don kurum yayi magana a kan sha’anin tsaro.

Sanata Shehu Sani yake cewa wani daga cikin Abokan aikin sa daga jihar Katsina ya taso masa haikan a Ranar Talata 30 ga Watan Afrilun 2019, saboda maganar da yake yawan yi a game da yadda halin tsaro ya tabarbare a Najeriya.

Shehu Sani ya kan yi magana a farfajiyar majalisa a game da yadda ake fama da kashe-kashe da kuma sace-sace, ana garkuwa da mutane a wurare da-dama a kasar. Wannan ne ya jawo masa suka wajen wani Sanata daga Katsina.

‘Dan majalisar yake bada labari cewa sai da ta kai shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya sa masu baki a lamarin, yana mai cewa Sanatan na da hakkin magana. Sani yace babu abin da zai sa yayi gum muddin ana kashe mutane.

KU KARANTA: Matar El Rufai tace ya kamata a ba Mata 50% na mukamai a 2019

Rashin tsaro: Shehu Sani yace ba zai yi shiru yayin da ake kashe mutane ba

Sanata Shehu Sani ya na yawan kokawa a kan matsalar sha'anin tsaro
Source: Depositphotos

Fitaccen Sanatan wanda ya tsere daga jam’iyyar APC mai mulki a bara ya bayyana cewa bai tafi majalisar tarayya da nufin yayi tsit yayin da ake kashe mutanensa ba. Sanatan duk ya bada wannan labari ne a shafin sa na sadarwa na Tuwita.

A wata magana da Sanatan yayi duk a shafin na sa, ya bayyana cewa rahoton da ke nuna cewa an kashe fiye da mutum 1, 000, sannan kuma an sace kusan 700 a cikin watanni 4 a Najeriya ya nuna cewa kasar tana cikin wani hali na uwar-bari.

Kwanan nan ne Sanatan ya bayyana yadda shi da wasu Sanatoci musamman na yankin Kano su kayi kokari a majalisar dattawa wajen ganin Budurwar nan da aka tsare a Kasar Saudi da sharrin sufurin kwayoyi ta fito daga cikin gidan yari.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel