Gwamnatin mu ta shirya biyan N30,000 mafi karancin albashin ma'aikata a Kano - Ganduje

Gwamnatin mu ta shirya biyan N30,000 mafi karancin albashin ma'aikata a Kano - Ganduje

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ta jaddada kudirin ta na fara biyan sabon mafi karancin albashi na Naira dubu talatin ga ma'aikatan gwamnati a fadin jihar.

Da sanadin jaridar Vanguard gwamnatin ta bayyana cewa, ta kammala duk wasu shirye-shiryen ta na tabbatar da kudirin fara biyan Naira dubu talatin a matsayin sabon mafi karancin albashi da ya yi daidai da amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Gwamnatin mu ta shirya biyan N30,000 mafi karancin albashin ma'aikata a Kano - Ganduje

Gwamnatin mu ta shirya biyan N30,000 mafi karancin albashin ma'aikata a Kano - Ganduje
Source: Twitter

Gwamna Ganduje da ake yiwa lakabi da Khadimul Islama, wato mai yiwa addinin Musulunci hidima, ya bayyana hakan ne cikin jawaban sa yayin taron bikin murnar ranar ma'aikata da aka gudanar a harabar filin wasanni na Sani Abacha da ka tantagwaryar birnin Kano.

Yayin ci gaba watsa kalamai ga wakilan kungiyar kwadago da suka halarci taron, gwamna Ganduje ya bayyana yadda gwamnatin sa ta zage dantse wajen ci gaba da inganta jin dadin ma'aikatan gwamnati a jihar Kano.

KARANTA KUMA: 'Yan ta'adda sun kai farmaki kwalejin ilimi a jihar Taraba

Domin bunkasa kwazo da himmar ma'aikata wajen jajircewa yayin sauke nauyin da rataya a wuyan su, gwamna Ganduje ya yi fashin baki kan yadda gwamnatin sa ta yaye shamaki na bambamci tsakanin mataki na masu kwalin babbar difloma da kuma kwalin digiri.

Cikin na sa jawaban, shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Kano, Kwamared Kabiru Ado Minjibir, ya yabawa kwazon gwamna Ganduje tare da jajircewar gwamnatin sa da fafutikar ta wajen inganta jin dadin ma'aikata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel