Gwamnoni na taimaka ma rashin tsaro don samun Karin Kudaden Samar da Tsaron da Suke Karba – In ji Magu

Gwamnoni na taimaka ma rashin tsaro don samun Karin Kudaden Samar da Tsaron da Suke Karba – In ji Magu

Mukaddashin Shugaban Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Zagon Kasa da Laifukan Almundahana (EFCC), Ibrahim Magu yayi zargin cewa wasu gwamnonin jihohi a asirce suna na taimaka ma sha’anin rashin tsaro a matsayin dalilan samun Karin kudaden samar da tsaro da ake ba su.

Magu, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wata makala mai taken “Bukatar Yaki da Rashawa/Samar da Kudaden Gudanar da Ayukkan Ta’addanci a Najeriya” a wurin taron sanin makamar aikin da aka shirya ma sabbin gwamnoni da gwamnoni masu dawowa, a dakin taron Banquet dake Fadar Shugaban kasa a Abuja, yace ba ya da wata jayayya kan dokar da ta bada damar samar da kudaden samar da tsaro.

Ya shawarci gwamnonin cewa dole ne su san akwai bukatar bayyana mamutane ake kashe dukiyoyinsu.

Kamar yadda yace “kuma mun ga shaidar satar dukiyoyin al’umma da wasu gwamnonin jihohi suka yi.

“Rashin tsaro ya samar da muhimmin abunda zai rayar da rashawa, kamar yadda shaida ta gabata a wata almundahanar dalar Amurka billiyan 2.1 ta samar da makamai wanda ya shafi manyan kwamandodin soja masu ritaya da wadanda ke cikin aiki."

Yace ba za a iya raba cin hanci da matsalar ta’addancin da ake fama da ita a Arewa maso yamma ba, ya kara da cewa yawan talauci dake faruwa sanadiyar ayukan rashawar da manyan mutane ke gudanarwa, za a iya cewa yana saukaka hanyar da ‘yan ta’adda ke daukar mayaka don tabbatar da tursasawar da suke wa gwamnatin Najeriya.

Shugaban hukumar yaki da rashawa ya kara bayyana cewa aikin ‘yan bindiga a yankin Naija Delta da aikin ta’addanci a Arewa maso yamma duk rashawa ke hadda su.

KU KARANTA: Martanin Shugaba Buhari ga Atiku: Ban bada kwangilar buga takardun zabe ba ga dan jam'iyyar APC

Yace, “A matsayina na mai bincike, na kadu ainun game da irin dukiyar da mutanen dake kula da gudanar da Hukumar Bunkasa Yankin Naija Delta (NDDC) suka sace. Abun takaici ne a ce wai har mai yi ma tsohon shugaban hukumar hidima an same shi da satar sama da naira biliyan ukku.”

Don haka ya shawarci sabbin gwamnoni da masu dawowa kan bukatar dake akwai ta kauce ma rashawa. Yace, “ko muna so ko ba muso,rashawa da ta’addanci sun zama dan juma da dan jumai, suna lahani ga kokarin da muke na mayar da Najeriya sahihiyar babbar kasa."

Ya kara da cewa kasawar Najeriya na amfana da albarkatun kasarta ana iya danganta ta da rashawa saboda ma’aikatan gwamnati nada dabi’a cigaba da satar dukiyoyin al’umma.

Magu yace kasar nan tayi asarar tiriliyoyin nairori a sanadiyyar rashawa, tare da bayanin cewa nazari kan dukiyoyin da Hukumar EFCC ta kama tun daga shekarar 2017 zuwa yanzu ya nuna cewa a shakarar 2017, EFCC ta kama Naira biliyan 473.065, Dalar Amurka miliyan 98, Euro miliyan 7 da Fam miliyan 294,000, yayin da aka kama Naira biliyan 236.16 a cikin shekarar 2018, wannan ya bada haske kan dukiyoyin da aka sace.

Shugaban hukumar ta EFCC ya bayyana cewa alakar dake tsakanin rashawa da ta’addanci ita ce rashawa na taimakama rashin tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel