Yanzu Yanzu: Yan sanda sun karyata batun sace dalibai a makarantar mata na Zamfara

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun karyata batun sace dalibai a makarantar mata na Zamfara

Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta karyata rahotannin da ke ikirarin cewa yan bindiga sun kai hari makarantar mata a garin Moriki da ke jihar Zamfara, sannan sun sace wasu dalibai.

Rundunar tace tawagarta na PMF/CTU/ da jami’an JTF karkashin jagorancin DPO sun je makarantar sun kuma yi arangama da yan bindigan sannan suka hana su samun shiga dakunan kwanan dalibai.

Mohammed Shehu, jami’in hulda da jama’a na rundunar, a wani jawabi da aka aikewa Legit.ng, rundunar tace: “DPO Zurmi ya samu kira cewa wasu yan bindiga sun shiga makarantar sakandare na mata Moriki da kekaramar hukumar Zurmi ta bangon bayan makarantar sannan suka yunkurin kai hari da sace dalibai.

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun karyata batun sace dalibai a makarantar mata na Zamfara

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun karyata batun sace dalibai a makarantar mata na Zamfara
Source: UGC

“A take, tawagar hadin gwiwa na PMF/CTU/ da jami’an JTF karkashin jagorancin DPO sun je makarantar sun kuma yi arangama da yan bindigan sannan suka hana su samun shiga dakunan kwanan dalibai, sai suka tsere zuwa daji.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Mahukunta a kasar Saudiyya sun sako Ibrahim Abubakar

“Babu daliba da aka sace kamar yadda wasu kafofin watsa labarai suka rahoto. Sai dai, daga bisani ba a ga wasu masu girki 2 da yaransu 3 ba.

“Yan sandan tare da hadin gwiwar hukumar makarantar na neman inda mutanen da aka rasa suke. Don kawo karshen haka, tawagar ceto da bincike sun rarrabu zuwa dajunan da ke kewaye da makarantar.

“A halin yanzu, an karfafa tsaro a makarantar da kewayenta domin guje ma ci gaba da afkuwar hakan."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel