Ministan Buhari yayi bayanin dalilinsa na rashin halartan gangamin ranar ma’aikata

Ministan Buhari yayi bayanin dalilinsa na rashin halartan gangamin ranar ma’aikata

Ministan kwadago da diban ma’aikata, Chris Ngige, ya bayyana cewa bai samu halartan gangamin bikin ranar ma’aikata ba saboda rashin lafiya.

Ministan ya kuma caccaki jawabin Shugaban kungiyar kwadago na Najeriya akan rashin hallaran nasa wajen bikin ranar ma’aikatan.

A wani jawabi daga mai bashi shawara na musamman a kafofin watsa labarai, Nwachukwu Obidiwe, ministan yace: “Sabanin rashin wayewa da karairayin da ke kunshe a cikin jawabin shugaba kungiyar kwadago na Najeriya, Ayuba Wabba, ina fatan fitar da shakku cewa ministan kwadago da diban ma’aikata, Ngige bai halarci gangamin ranar ma’aikata ba wanda aka gudanar a ranar 1 ga watan Mayu saboda dalilai na rashin lafiya."

Ministan Buhari yayi bayanin dalilinsa na rashin halartan gangamin ranar ma’aikata

Ministan Buhari yayi bayanin dalilinsa na rashin halartan gangamin ranar ma’aikata
Source: Depositphotos

Jawabin yace ministan na kwance saboda zazzabin mura da yayi masa kamu tun ranar Lahadin da ya gabata, inda ya kara da cewa “ya gana da likitocinsa a ranar Litinin da ya gabata sannan tun lokacin yana gida inda yake samun lafiya."

KU KARANTA KUMA: An harbi sufeto yayinda yan sanda ke musayar wuta da wadanda suka sace surukin Buhari

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Ministan kwadago na Najeriya Dakta Chris Ngige, ya bata bat yayin murnar bikin ranar ma'aikata da aka gudanar a ranar 1 ga watan Mayun 2019 cikin harabar taro ta Eagle Square da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Wannan shi ne karo na farko cikin shekaru aru-aru a tarihin Najeriya da Ministan kwadagon kasar zai kauracewa halartar bikin murnar ranar ma'aikata da aka saba gudanar wa a ranar 1 ga watan Mayun ko wace shekara bisa al'ada.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel