Gwamnan Ebonyi ya sallami jami’ai 824

Gwamnan Ebonyi ya sallami jami’ai 824

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi yayi umurnin sallamar manyan jami’ansa guda 824 cikin gaggawa.

Wadanda yayi umurnin sallama sun hada da manyan hadimai na fasaha 560, jagororin cibiyoyin ci gaba 64 da kuma manajojin kwamiti 200 a jihar.

Wani jawabi daga babban sakataren gwamnan, Clement A Nweke, yace sallaman ya fara aiki daga jiya Laraba, 1 ga watan Mayu.

Ya bayyana cewa: “Gwamna David Nweze Umahi, ya amince da rushe jagororin kwamiti 64 da manyan hadimansa na fasaha daga ranar 1 ga watan Mayu, 2019.

Gwamnan Ebonyi ya sallami jami’ai 824

Gwamnan Ebonyi ya sallami jami’ai 824
Source: Twitter

“Yayi umurnin cewa dukkanin ma’aikatan gwamnati da abun ya shafa su gabatar da dukkanin kayayyakin gwamnati da ke a hannunsu zuwa ga babban sakataren gwamna a ranar 1 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: An harbi sufeto yayinda yan sanda ke musayar wuta da wadanda suka sace surukin Buhari

“Yana masu fatan alkhairi sannan yayi alkawarin gayyatarsu wani taro n murna domin yaba masu kwanan nan."

A wani laamari na daban, Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnatin jihar Kano ta soke banbancin da ke tsakanin HND da digiri a jihar.

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya bayyana hakan a bikin ranar ma’aikata wanda aka gudanar a babban filin wasa na Sani Abacha a ranar Laraba, 1 ga watan Mayu a Kano. Ganduje yayi bayanin cewa an kammala duk wani shirye-shirye don fara biyan sabon mafi karancin albashi na N30,000 wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shi.

A cewar Ganduje, gwamnatinsa za ta ci gaba da ba jin dadin ma’aikatar gwamnati muhimmanci da dukkanin mazauna jihar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel