'Yan ta'adda sun kai farmaki kwalejin ilimi a jihar Taraba

'Yan ta'adda sun kai farmaki kwalejin ilimi a jihar Taraba

Daya daga cikin daliban kwalejin ilimi ta Zing da ke jihar Taraba, ya riga mu gidan gaskiya yayin da wasu 'yan ta'adda da su ka saba addabar dalibai su ka kai farmaki cikin makarantar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar rahoton ta bayyana cewa, mummunar ta'ada gami da zalunci ya sanya a karo daban-daban 'yan ta'adda daga garin Zing sun saba addabar daliban kwalejin ilimi wajen kai masu hare-hare ba tare da wani hakki ba.

Gwamnan jihar Taraba; Ishaku Darius

Gwamnan jihar Taraba; Ishaku Darius
Source: Twitter

Yayin da tura ta kai bango wajen mayar da martanin wannan cin kashi na ba bu gaira ba bu dalilin sa, daya daga cikin daliban kwalejin ya riga mu gidan gaskiya.

Sai dai rahotanni sun bayyana cewa, harsashin bindiga na jami'an tsaro da suka ketaro daga birnin Jalingo ke da alhakin katse hanzarin wannan dalibi yayin yunkurin su na kwantar da tarzoma.

KARANTA KUMA: Kungiyar kwadago ta yiwa Ministan kwadago kaca-kaca

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Taraba, DSP David Misal, ya bayar da shaida ta tabbatar aukuwar wannan mummunan lamari yayin da manema labarai su ka nemi jin ta bakin sa. Ya ce tuni komai ya lafa kuma al'amurra sun ci gaba da gudana kamar yadda aka saba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel