Hadiza El-Rufai tana so Mata su rike rabin mukaman da ke Gwamnati a 2019

Hadiza El-Rufai tana so Mata su rike rabin mukaman da ke Gwamnati a 2019

Jaridar Daily Trust ta rahoto Uwargidar gwamnan jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Nasir El-Rufai, tana kira na a samu mata da-dama a cikin sabuwar gwamnatin da za a kafa a tsakiyar shekarar nan ta 2019.

Uwargidar gwamnan ta jihar Kaduna ta fito ta bayyana cewa ya kamata a warewa Mata kashi 50% na mukaman da ake da su a gwamnati. El-Rufai tace akwai bukatar Mata su rika shiga cikin gwamnati domin a dama da su.

Matar gwamnan take cewa idan aka duba yawan Mata da ke cikin al’umma a yau, za a ga cewa kusan yawan su daya da maza, don haka tace babu abin da ya kamata ya hana a rika yin raba-daidai tsakanin Mata da Maza a yanzu.

KU KARANTA: Tsohon Kwamishinan Kaduna ya fara neman aiki-yi bayan an sallame sa

Hadiza El-Rufai tana so Mata su rike rabin mukaman da ke Gwamnati

Mai dakin El-Rufai ta na so Mata da Maza su rika yin raba daidai
Source: Twitter

Hadiza El-Rufai tayi wannan kira ne a lokacin da ta halarci liyafar ban-kwanan da Matan da su kayi aiki da gwamnatin jihar Kaduna su ka shirya. El-Rufai ta nuna godiya da yabo ga wadannan Mata da su kayi wa jihar ta Kaduna hidima.

Mai dakin Gwamna El-Rufai take cewa Mata za su cigaba ne kawai idan ana ba su dama su na gurzawa har su fito da kan-su. Matar Mai girma gwamnan ta kuma yi kira ga ‘yan uwan na ta Mata da su zama masu hadin-kai a tsakanin su.

Kwamishinar harkokin mata na jihar, Hajiya Hafsat Baba, tana cikin wadanda su kayi magana a wajen wannan biki inda ta godewa gwamna da ya yarda da ita, kuma ya ba ta dama. Wata Kwamishinar, Ruth Alkali, ita ma tayi na ta jawabin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel