An harbi sufeto yayinda yan sanda ke musayar wuta da wadanda suka sace surukin Buhari

An harbi sufeto yayinda yan sanda ke musayar wuta da wadanda suka sace surukin Buhari

Rundunar yan sandan Katsina ta bayyana cewa tawagarta a yankin Kusada sun kama sannan sun yi musayar wuta da wadanda suka yi garkuwa da Magajin Garin Daura wanda yayi sanadiyar harbin wani Sufeto Muntari Maikudi, jami’in dan sandan sashin.

Kakakin rundunar, SP Gambo Isah a wani jawabi da ya saki kan sace basaraken a safiyar yau Alhamis, 2 ga watan Mayu yace jami’in dan sandan ya samu rauni na harbi sannan anyi gaggawan kai shi babban asibitin tarayya na Katsina domin samun kulawar likita.

A cewarsa, tawagar Sufeto Janar na yan sanda, tawagar SARS, da sashin kula da ta’addanci sun rigada sun bazama domin ceto basaraken a raye cikin koshin lafiya.

An harbi sufeto yayinda yan sanda ke musayar wuta da wadanda suka sace surukin Buhari

An harbi sufeto yayinda yan sanda ke musayar wuta da wadanda suka sace surukin Buhari
Source: UGC

“Rundunar na kira ga jama’a das u taimaka wa hukumomin tsaro a koda yaushe kan lokaci da kuma bayar da bayanai kan ayyukan yan bindigan. Ku sani cewa hukumomin tsaro na iya bakin kokarinsu don kawo karshen ayyukan ta’addanci,” inji shi.

KU KARANTA KUMA: Ranar ma’aikata: Gwamnatin Kano ta kawo karshen banbancin da ke tsakanin Digiri da HND

Yace wasu yan bindiga su shida sun zo suna harbi a iska sannan suka kai farmaki gidan Magajin Garin Daura, Alh Musa Uba a mota kirar Peugeot 405, mara rijista, kalar bula sannan suka sace shi yayinda yake zaune a kofar gidansa zuwa wani wuri da ba a sani ba.

“Nan take kwamishinan yan sandan jihar Katsina, CP Sanusi Buba, tare da tawagar yan sanda suka isa wajen da abun ya faru,” inji shi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel