Sanata Sani ya bayyana yadda za a tsere ma makircin masu dasa miyagun kwayoyi a filin jirgin sama

Sanata Sani ya bayyana yadda za a tsere ma makircin masu dasa miyagun kwayoyi a filin jirgin sama

Sanata Shehu Sani ya shawarci matafiya kan yadda za su tsere ma fadawa tuggun makiran filin jirgin sama da ke dasa miyagun kwayoyi a jakar fasinjoji.

Sanatan mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, ya bayar da shawarar ne a shafin Twitter a ranar Laraba, 2 ga watan Mayu.

Shawarar na zuwa ne kan batun sakin Zainab Aliyu da Ibrahim Abubakar wadanda ma’aikatan filin jirgin sama na Kano suka shirya wa tuggu.

Tuni dai an saki mutanen biyu bayan gwamnatin tarayya ta sanya baki a lamari.

Sanata Sani ya bayyana yadda za a tsere ma makircin masu dasa miyagun kwayoyi a filin jirgin sama

Sanata Sani ya bayyana yadda za a tsere ma makircin masu dasa miyagun kwayoyi a filin jirgin sama
Source: Depositphotos

Bayaninsa: “Idan za ku yi tafiya ciki ko wajen kasar, kuyi amfani da wayarku don daukar biydiyon jakunkunan da za ku auna a filin jirgi, don kare kanku daga wadanda ke kasuwanci da shirya tuggu.”

KU KARANTA KUMA: Ranar ma’aikata: Gwamnatin Kano ta kawo karshen banbancin da ke tsakanin Digiri da HND

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa kwana guda bayan sakin Zainab Habibu Aliyu da aka tsare a Saudiyya bisa zargin safarar miyagun kwayoyi, mahukunta kasar sun sake sakin wani mutum mai suna Ibrahim Abubakar wadda shima ya kasance a tsare.

An mika Abubakar a hannun wakilin ofishin jakadancin Najeriya, Jeddah Garba kamar yadda TVC News ta ruwaito.

An tsare Ibrahim Abubakar ne bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar mai tsarki kamar yadda ya faru da Zainab Aliyu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel