'Yan bindiga sun sace mutane 30 a harin da suka kai ranar Asabar - Basaraken Zamfara

'Yan bindiga sun sace mutane 30 a harin da suka kai ranar Asabar - Basaraken Zamfara

Sarkin Bungudu na Jihar Zamfara, Alhaji Hassan Attahiru ya ce 'yan bindigan da suka kai hari garin sa a ranar Asabar da sunyi awon gaba da mutane 30 ne.

A hirar da sarkin ya yi da jaridar Punch a ranar Talata, ya ce sojojin saman Najeriya, (NAF) ba su amsar kirar neman dauki da akayi musu ba a ranar da 'yan bindigan suka kai hari a garinsa suka kashe mutum 15 a ranar Asabar sai dai NAF din ta ce akwai mikirci cikin kalaman na basaraken.

Amma a ranar Laraba 1 ga watan Mayu basaraken ya yabawa kafafen yada labarai bisa gudunmawar da su keyi na bayyana halin rashin tsaro da ake fama da ita a masarautarsa.

'Yan bindiga sun sace mutane 30 a harin da suka kai ranar Asabar - Basaraken Zamfara

'Yan bindiga sun sace mutane 30 a harin da suka kai ranar Asabar - Basaraken Zamfara
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Tsallake rijiya da baya: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan Zainab Aliyu

Ya ce, "Lamarin ya yi muni har ta kai ga cewa al'umma ta suna gargadi na kada in ziyarci wasu wurare domin suna fargabar 'yan bindiga za su sace ni.

"Baya ga mutane 15 da 'yan bindiga suka kashe a harin da suka kai a kauyen Makwa, sun kuma yi awon gaba da wasu mutane 30 zuwa wani wurin da ba a sani ba.

"Akwai yiwuwar za su sako su idan an biya kudin fansa duk da cewa gwamnatin jihar ba ta goyon bayan biyan kudin fansar."

A kan ikirarin da jami'an tsaro na Opertaion Sharan Daji da Harbin Kunama III su kayi na cewa sun bi sahun 'yan bindigan sun ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su, basaraken ya fadawa jami'an tsaron su dena fadin abinda ba su aikata ba.

Ya ce, "Wadanda suka yi ikirarin cewa sun ceto daga wurin masu garkuwa da mutanen sun hadu da su ne a hanyarsu ta dawowa gida. Ba suyi wata artabu da 'yan bindigan ba.

"Akwai wuraren da 'yan bindigan suka kafa sansaninsu tun shekaru hudu da suka gabata kuma har yanzu ba su canja wuri ba.

"Jami'an tsaro sun san wannan bayannan saboda an dade da fada musu amma ba su amfani da bayyanan.

"Idan matsalar su rasa jam'ansu ne sai su amsa hakan domin mu zauna mu tattauna a kan batun. Abin takaici shine babu hadin kai tsakanin jami'an tsaro da al'ummar da suka fi sannin garin."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel