Duk wanda yaji labarin ana daukar aiki, ya sanar da ni – Sani Dattijo

Duk wanda yaji labarin ana daukar aiki, ya sanar da ni – Sani Dattijo

Yayin da ake shirin kafa sabon gwamnati a Najeriya, masu mulki da-dama sun saukar da dukkanin mukarrabansu domin shiryawa shigowar gwamnati mai zuwa a Ranar 29 ga Watan Mayun gobe.

A jihar Kaduna, tuni gwamna Malam Nasir El-Rufai ya umarci kaf Kwamishinoninsa, da masu ba sa shawara da kuma masu taimaka masa wajen aiki da su sauka daga matsayin da su ke kai a kokarin da yake yi na kafa sabon gwamnati.

Daya daga cikin manyan Kwamishinonin gwamna mai-ci Nasir El-Rufai a jihar Kaduna, Muhammad Sani Dattijo ya rubuta takardarsa na murabus, wanda ya rattabawa hannu kuma ya aikawa mai girma gwamna kamar yadda yace.

KU KARANTA: Babban Gwamnan APC ya nuna dar-dar game da yin karin albashi

Duk wanda yaji labarin ana daukar aiki, ya sanar da ni – Sani Dattijo
Dattijo yana rahar neman aikin yi daga sauka daga mukamin Kwamishina
Source: Instagram

Malam Muhammad Sani Dattijo wanda shi ne Kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na jihar Kaduna ya bayyana wannan ne a shafin sa na sadarwa Tuwita. Kwamishinan bai tsaya nan ba inda yace yana neman inda ake daukar aiki.

Kwamishinan kasafin yake cewa shi tsohon Ma’aikacin gwamnati ne wanda ya kware wajen amfani da manhajar Mircrosoft Excel da Power Point, Sani Dattijo ya nemi jama’a su aika wannan sako na sa ko ina, ko za a samu ya dace.

Wannan Matashi da ya rike Kwamishina a gwamnatin jihar Kaduna, kwararre ne a harkar ilmin tattalin arziki, har ya kuma yi aiki a majalisar dinkin Duniya. Don haka ake tunanin cewa yana cikin wadanda gwamna zai sake komawa da su.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel