Ranar ma’aikata: Gwamnatin Kano ta kawo karshen banbancin da ke tsakanin Digiri da HND

Ranar ma’aikata: Gwamnatin Kano ta kawo karshen banbancin da ke tsakanin Digiri da HND

Gwamnatin jihar Kano ta soke banbancin da ke tsakanin HND da digiri a jihar. Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya bayyana hakan a bikin ranar ma’aikata wanda aka gudanar a babban filin wasa na Sani Abacha a ranar Laraba, 1 ga watan Mayu a Kano.

Ganduje yayi bayanin cewa an kammala duk wani shirye-shirye don fara biyan sabon mafi karancin albashi na N30,000 wanda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da shi.

A cewar Ganduje, gwamnatinsa za ta ci gaba da ba jin dadin ma’aikatar gwamnati muhimmanci da dukkanin mazauna jihar.

Mista Kabir Ado-Minjibir, Shugaban kungiyar kwadago na jihar Kano, ya yaba ma kokarin gwamnatin jihar waje inganta jindadi da yanayin aikin ma’aikatan gwamnati.

Ranar ma’aikata: Gwamnatin Kano ta kawo karshen banbancin da ke tsakanin Digiri da HND
Ranar ma’aikata: Gwamnatin Kano ta kawo karshen banbancin da ke tsakanin Digiri da HND
Asali: Twitter

Ya roki gwamnatin jihar da ta fara biyan alawus na ma’aikatan jami’ar jihar kamar yadda ake yi ga takwarorinsu na gwamnatin tarayya.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Katsina ya nuna rashin tabbass kan biyan mafi karancin albashi N30,000

Shugaban kungiyar ta NLC ya kuma yaba ma gwamnatin kan tabbatar da biyan albashin ma’aikata ba tare da jinkiri bad a kuma biyan yan fansho.

Ado-Minjibir ya bukaci ma’aikatan gwamnati da su biya karamcin gwamnatin ta hanyar yin aiki yadda ya kamata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel