Kuyi koyi da Buhari – Nuhu Ribadu yayi kira ga sabbin gwamnoni

Kuyi koyi da Buhari – Nuhu Ribadu yayi kira ga sabbin gwamnoni

Tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Malam Nuhu Ribadu ya shawarci sababbin gwamnonin Najeriya da suyi koyi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a salon mulkinsu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ribadu ya bayyana haka ne yayin taron samun horo da kungiyar gwamnonin Najeriya ta shirya ma sabbin gwamnoni da masu zarcewa a ranar Talata, 30 ga watan Afrilu a Abuja, inda aka gayyaceshi a matsayin bako na musamman.

KU KARANTA: Siyasa mugun wasa: Atiku ya kalubalanci Buhari ya bayyana shaidar kammala karatu

Kuyi koyi da Buhari – Nuhu Ribadu yayi kira ga sabbin gwamnoni
Nuhu Ribadu
Asali: UGC

Nuhu Ribadu yayi kira ga sababbin gwamnoni da suyi koyi da salon mulkin shugaba Buhari ta yadda yake bambamta sha’anin mulki da jagoranci da kuma bukatar kashin kansa, hakan yasa aka yi masa shaidar baya satar kudin gwamnati.

“Kun yi sa’a kuna da wanda zaku yi duba a gareshi kamar Buhari, don haka nake rokonku daku daure kuyi koyi da shugaban kasa Muhammadu Buhari, bashi da wani abokin huldar kasuwanci, baya zama da kowa wai don kulla wata cinikayya.

“Buhari bai sake siyan wani gida ko kadara ba tun daya sake dawowa a matsayin shugaban kasar Najeriya a karkashin tsarin Dimukradiyya, don haka aka daina samun attajirai biloniya da babu wanda ya san sana’arsu, tabbas Buhari shugaba ne nagari abin koyi.” Inji Nuhu Ribadu.

Idan za’a tuna Nuhu Ribadu ya rike EFCC ne daga shekarar 2003 zuwa 2007, inda daga nan ya tsaya takarar shugabancin Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyar ACN a shekarar 2011, sa’annan ya tsaya takarar gwamnan jahar Adamawa a inuwar lemar PDP a 2015, ya sake tsayawa takarar gwamnan Adamawa a inuwar APC a zaben 2019, amma bai kai labari ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel