Zan zamo gwamna na farko da zai biya karancin albashi N30,000 - Yari
Gwamna Abdul’aziz Yari na jihar Zamfara a jiya Laraba, 1 ga watanMayu yace shine zai zamo gwamna na farko a kasar da zai fara biyan N30,000, sabon mafi karancin albashi.
Da yake Magana a bikin ranar ma’aikata a garin Gusau, Yari ya gargadi ma’aikata akan sanya matayensu da yaransu a takardar biyan albashin.
Da ya samu wakilcin babban sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Muhammad Shinkafi, Yari yace: "Zai zama rashin adalci idan ma’aikatan gwamnati suka sanya matayensu da kananan yara a takardar biyan albashin kuma hakan zai shafi isar da aiki ga al’umma da yawa.”
Yari yace zai magance batun kudin sallamar ma’aikata kafin ya bar kujerar mulki.

Asali: UGC
Shugaban kungiyar kwadago na jihar, Bashir Marafa, ya bukaci gwanatin jihar da ta cika dukkanin alkawaran da ta daukar ma ma’aikata.
KU KARANTA KUMA: El-Rufai da Fayemi na tseren neman kujerar Yari na Shugaban kungiyar Gwamnoni
A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, a Jihohin Legas, Osun, Taraba da kuma Sokoto, haka aka yi taron bikin Ranar Ma’aikata a Najeriya, ba tare da an san inda gwamnonin su ka sa gaba ba, a game da maganar karin albashin ma’aikata.
Daily Trust ta rahoto cewa wasu daga cikin gwamnoni ba su bayyana inda su ka sa dosa ba a kan maganar kara albashin ma’aikatan gwamnati zuwa akalla N30, 000 duk wata. Daga cikin wadannan gwamnoni akwai na Legas.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng