Yahaya Bello ya kai wa Tinubu ziyara a gidansa na Abuja

Yahaya Bello ya kai wa Tinubu ziyara a gidansa na Abuja

Jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello a gidansa da ke babban birnin tarayya, Abuja a ranar Litinin 30 ga watan Afrilun 2019.

Gwamna Bello ya kai wannan ziyarar ne a yayin da wasu ke yada jita-jitar cewa rikici ya barke tsakaninsa da jagoran na jam'iyyar ta APC.

A makon da ta gabata, kafafen yada labarai da dama sun wallafa rahoto da ke cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar APC karkashin jagorancin Tinubu suna shirin hana Gwamna Bello tikitin takarar gwamna a zaben da za a gudanar a jihar Kogi a watan Nuwamba.

Yahaya Bello ya kaiwa Tinubu ziyara a gidansa na Abuja

Yahaya Bello ya kaiwa Tinubu ziyara a gidansa na Abuja
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Wani gurgu maras kafafu ya kammala digiri a ABU da sakamako mafi daraja

Rahoton ya ce gwamna Bello baya ga maciji da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar sai dai hadimin gwamnan a fanin kafafen yada labarai ya karyata wannan rahoton.

Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas na hannun daman shugaban jam'iyyar APC na kasa ne Kwamared Adams Oshiomhole.

Hakan yasa ake ganin yana da ikon zartas da wasu abubuwa a jam'iyyar saboda kusancinsa da Oshiomhole.

Ba a san takamamen abinda suka tattauna a ganawar ba sai dai wani wanda ya hallarci taron ya shaidawa Legit.ng cewa 'ziyarar ban girma ne kawai.'

"Gwamnan ya gana da Tinubu a wurin taron kungiyar gwamnoni kuma jagoran jam'iyyar na kasa ya bukaci ya ziyarce shi a gidansa.

"Gwamnan ya amsa gayyatar Tinubu kasancewar dan jam'iyya mai biyaya da girmama na gaba da shi. Jagoran jam'iyyar na kasa ya bukaci gwamnan ya yi aiki tare da shugabanin jam'iyyar APC a jiharsa domin samun nasarara a zaben da ke tafe," a cewar majiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel