Hotuna: - Karuwai sun fito murnar ranar ma'aikata

Hotuna: - Karuwai sun fito murnar ranar ma'aikata

Mata masu zaman kansu suma sun fito murnar ranar maa'aikata da aka gabatar jiya Laraba a fadin Najeriya

A daidai lokacin da ma'aikata ke faman bikin murnar ranar ma'aikata a Najeriya, sai ga kungiyar mata masu zaman kansu suma sun hado na su gangamin domin nuna murnar su a wannan ranar

Matan wadanda suka fito dauke da hotuna masu rubutu da ke nuna cewar suma suna da 'yanci kuma yau ranar su kamar yadda kowane ma'aikaci ya ke murna da wannan rana.

Mata masu zaman kansu suna fuskantar kalubale bale da yawa a Najeriya, musamman ma a yankin arewacin kasar, inda suke ganin hakan ya sabawa addini da al'ada.

Hotuna: - Karuwai sun fito murnar ranar ma'aikata

Hotuna: - Karuwai sun fito murnar ranar ma'aikata
Source: Facebook

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya sake magana akan sabon albashi

Ranar Talatar da ta gabata ne majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku cewa hukumar Hisba ta jihar Kano ta tashi tsaye wurin kame dukkanin mata masu zaman kansu a fadin jihar saboda zuwan azumin watan Ramadana na wannan shekara.

Sannan kuma idan ba a manta ba ranar Asabar dinnan da ta gabata majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku labarin yadda jami'an 'yan sanda suka kai samame wasu wurin casu dake cikin birnin Abuja inda suka kama karuwai kimanin guda 70.

Sai dai kuma hakan ya kawo kace-nace a shafukan sada zumunta na zamani, inda wasu ke ganin hakan bai kamata ba, saboda hakan shine hanyar da matan ke samun na abinci, bisa la'akari da rashin aikin yi da ya addabi kasar.

Hotuna: - Karuwai sun fito murnar ranar ma'aikata

Hotuna: - Karuwai sun fito murnar ranar ma'aikata
Source: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel