El-Rufai da Fayemi na tseren neman kujerar Yari na Shugaban kungiyar Gwamnoni

El-Rufai da Fayemi na tseren neman kujerar Yari na Shugaban kungiyar Gwamnoni

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da takwaransa na jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi na takarar neman kujerar Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya.

Amma akwai alamu da ke nuna cewa dan takarar na kudu maso yamma na iya samun kujerar tunda Shugaban kungiyar mai barin gado, Gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari dan arewa ne.

Sai dai ance El-Rufai yace lallai sai ya nemi matsayin sannan har yanzu bai yarda ya janye w kowani takwaran nasa ba.

Kungiyar dai ta samu shugabanni shida tun shekaru 20 da ya gabata lokacin da kasar ta koma kan tafarkin damokradiyya.

El-Rufai da Fayemi na tseren neman kujerar Yari na Shugaban kungiyar Gwamnoni

El-Rufai da Fayemi na tseren neman kujerar Yari na Shugaban kungiyar Gwamnoni
Source: UGC

Tsoffin shugabannin kungiyar sune, Alh. Abdullahi Adamu (Nasarawa, 1999 – 2004), Arc. (Obong) Victor Attah, (Akwa Ibom 2004 -2006), Chief Lucky Igbinedion (Edo 2006 – 2007), Dr. Abubakar Bukola Saraki, (Kwara 2007- 2011) Rotimi Amaechi ( Rivers 2011 -2015) da kuma Abdulaziz Yari(2015-2019).

A cewar majiyoyi, zaben kungiyar gwamnonin Najeriya zai gudana a ranar 22 ga watan Mayu a Abuja gabannin taron tattalin arzikin kasa na karshe ga gwamnoni masu barin gado a ranar 23 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: An kashe wasu ‘Yan bindiga a bakin fadar Sarkin Birnin Magaji

An tattaro cewa gwamnonin sun fara tuntubar juna kan wanda za su zaba a matsayin shugabansu saboda baabban aiki da ke gabansu, ciki harda bukatar wanzar da alaka mai kyau tare da Shugaban kasa; biyan mafi karancin albashi 30,000 da kuma fa’idarsa kan tattalin arzikin jihohin; hauhawan kalubalen tsaro; da kuma nean sabon hanyat daukar nauyin karatu.

Wani gwamna daga Arewa ta tsakiya yace: “Gwamnoni da dama na son shugabancin kungiyar gwamnonin Najeriya, amma yanzu an bar mu da zabi biyu - el-Rufai da Fayemi."

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel