Sai na kashe Nnamdi Kanu - Asari Dokubo ya ci alwashi

Sai na kashe Nnamdi Kanu - Asari Dokubo ya ci alwashi

- Asari Dokubo ya ci alwashin kashe Nnamdi Kanu ko ta wane hali ne

- Ya ce bai ga dalilin da zai sa su dinga zubar da jinin 'yan uwansu a gwagwarmayar da suke yi ba

- Ya ce shi ma kwararre ne wurin kashe mutane

Tsohon shugaban kungiyar tsagerun Niger Delta, Asari Dokubo ya yi alkawarin kashe shugaban 'yan gwagwarmayar kafa yankin Biafra, Nnamdi Kanu.

Dokubo ya bayyana cewa, gwagwarmayar da 'yan kungiyar suke wurin ware yankin su na Biafra na samun matsala ne saboda shugaban na su Nnamdi Kanu. A cikin wani bidiyo da ya sanya a shafinsa na Facebook jiya Laraba, ya ce yana mamakin yadda aka yi Kanu ya gudu daga kasar nan maimakon ya zo ya kalubalanci gwamnatin Najeruya.

Sai na kashe Nnamdi Kanu - Asari Dokubo ya ci alwashi

Sai na kashe Nnamdi Kanu - Asari Dokubo ya ci alwashi
Source: Facebook

Ya kuma zargi Nnamdi Kanu da hannu wurin kashe babban Fasto Anthony Nwoko, inda ya bayyana cewa bai taba kashe kowa ba.

A bayanin da ya yi, ya ce, "Ya ku 'yan uwanmu na yankin Biafra, a daidai wannan lokaci da muke gwagwarmaya, rayukan 'yan uwanmu suke salwanta, domin kafa yankin mu, sai gashi wasu 'yan tsiraru suna amfani da wannan damar wurin ganin sun mulke mu. Amma saboda munyi imani da cewa ko ta halin kaka sai mun kafa yankin Biafra, sai ba mu ga irin wadannan munafukan mutanen da suke yi mana zagon kasa ba.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutaane sun bayyana dalilan da yasa suke satar mutane a kasar nan

Ya cigaba da cewam Nnamdi Kanu sai na kashe ka, ka kwana da sanin haka, saboda na kware wurin kashe mutane."

Asari Dokubo, yana magana ne akan kashe Fasto Nwoko, ya ce ba daidai ba ne ace suna kashe 'yan uwansu. Ya yi gargadin cewa ba zai ja da baya ba wurin kashe Nnamdi Kanu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel