Tabarbarewar tsaro: An nemi shugaba Buhari ya kaddamar da dokar ta baci a Najeriya

Tabarbarewar tsaro: An nemi shugaba Buhari ya kaddamar da dokar ta baci a Najeriya

Wata kungiya mai zaman kanta, gidauniyar Musulunci ta Al-furqan tayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari daya kaddamar da dokar ta baci a Najeriya bisa dimbin matsalolin tsaron da suka yi ma kasar daurin huhun goro a yanzu haka.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito guda daga cikin shuwagabannin kungiyar, Malam Nurudeen Asunogie ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 1 ga watan Mayu, inda yace akwai bukatar Buhari ya dauki wannan mataki duba da yawaitan kashe kashe da garkuwa da mutane da ake fama dasu a Najeriya.’

KU KARANTA: Gwamnoni na fakewa da matsalar tsaro suna satar kudaden al’umma – Inji Magu

Tabarbarewar tsaro: An nemi shugaba Buhari ya kaddamar da dokar ta baci a Najeriya

Tabarbarewar tsaro: An nemi shugaba Buhari ya kaddamar da dokar ta baci a Najeriya
Source: UGC

Malam Nurudeen yayi magana da yawun kungiyar ne bayan ta kammala wani babban taronta data gudanar a babban birnin tarayya Abuja, inda ta lissafa ma shugaban kasa wasu manyan ayyuka na musamman daya kamata ya mayar da hankali akansu.

“Babban lamarin daya kamata ka mayar da hankali a yanzu shine tsaro, saboda a gaskiya duk inda ka shiga a fadin Najeriya babu tsaro a yanzu haka, kusan ma muce tamkar wata kwarya kwaryan yakin basasa muke ciki.

“Don haka yan Najeriya suna bukatar mafita daga gareka, lokaci yayi daya kamata ka kaddamar da dokar ta baci, ka kuma baiwa shuwagabannin tsaro kwana 40 su fallasa tare da kama duk wasu masu daukan nauyi da shirya matsalolin tsaro a Najeriya.” Inji kungiyar.

Daga karshe Nurudeen ya tabbatar ma Buhari cewa yan Najeriya na tare dashi, kuma Allah na tare dashi, don haka zasu cigaba da tayashi da addu’ar cigaba da samun karin lafiya da samun nasara akan makiyan Najeriya gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel